Inna lillahi: Wani maigida ya yiwa matarsa yankan rago a jihar Katsina

Inna lillahi: Wani maigida ya yiwa matarsa yankan rago a jihar Katsina

Ana tuhumar wani mutumi mai matsakaicin shekaru mai suna, Yahaya, da zargin yiwa uwargidarsa, Hindatu Manaja, yankan rago sakamakon rashin jituwa da suke samu na zaman aure.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa wannan abu dai ya faru ne a daren Talata, 19 ga watan Maris, a Unguwar Babba, karamar hukumar Jibia dake jihar Katsina. Wannan abu ya tayar da hankalin jama'a.

An ga gawar Hindatu da safe cikin jini da yanka a wuyanta. Mahaifyarta, Fatima Yar Ma'aiki ce ta gani kuma ta kira jama'a har ya kai ga gayyatan jami'an yan sanda.

Ta ce Hindatu da mijinta sun samu sabani da mijin na tsawon lokaci yanzu kuma babban dalilin shine gazawarsa wajen sama musu abinci. Sabani tsakanin ma'aurata ba bakon abu bane amma bai kamata ya kai ga kisa ba.

Yayinda aka tuntubi kakakin hukumar yan sandan, SP Gambo Isah, ya yiwa manema labarai alkawarin yin bincike sannan ya bada rahoto.

A bangare guda, wasu mutanen kauye a karamar hukumar Birnin Gwari da jihar Kaduna sun gudu daga muhallansu da gonakinsu sakamakon hare-haren da yan bindiga ke cigaba da kawowa garuruwan da ke makwabtaka da su.

An tattaro cewa mutanen sun gudu daga garuruwan Kamfanin Doka, Goron Dutse, Irirori, Layin Mai Gwari da Kungi zuwa cikin garin Birnin Gwari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel