NNPC zata fadada bututun iskar gas daga Ajaokuta zuwa Kano zuwa kasar Aljeriya

NNPC zata fadada bututun iskar gas daga Ajaokuta zuwa Kano zuwa kasar Aljeriya

Babban manajan rukunin kamfanonin albarkatun man fetur na Najeriya watau Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC), Dakta Maikanti Baru, ya bayar da labarin cewa gwamnati zata fadada bututun iskar gas daga Ajaokuta zuwa Kano zuwa kasar Aljeriya.

Shugaban na NNPC ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar masu fasahar albarkatun man fetur ta kasa watau Petroleum Technology Association of Nigeria (PETAN) a ofishin sa a Abuja.

NNPC zata fadada bututun iskar gas daga Ajaokuta zuwa Kano zuwa kasar Aljeriya
NNPC zata fadada bututun iskar gas daga Ajaokuta zuwa Kano zuwa kasar Aljeriya
Asali: Twitter

KU KARANTA: Za'a kara haraji a 2019

Mai karatu dai zai iya tuna cewa bututun iskar gas din dai a baya mun baku labarin cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta bayar da kwangilar shinfida shi daga garin Ajaokuta dake jihar Kogi ya bi ta jihar Kaduna zuwa Kano dukkan su a Arewacin Najeriya.

Duk dai a game da albarkatun man fetur din, mai karatu zai iya tuna cewa tuni kamfanin na NNPC ya soma aikin fara hakar mai a jihar Gombe ta Arewacin Najeriya wanda yanzu haka aikin yayi nisa.

A wani labarin kuma, Mista Godwin Emefiele, shugaban babban bankin Najeriya watau Central Bank of Nigeria (CBN) ya bayyana cewa 'yan Najeriya na kashe kudaden da suka kai akalla Dalar Amurka miliyan dari biyar a duk shekara wajen shigo da man ja daga kasashen waje.

Shugaban Central Bank of Nigeria (CBN) din yayi wannan ikirarin ranar Litinin din da ta gabata da yake jawabi a wajen wani taron masu ruwa da tsaki na masu sana'ar man ja a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel