Zaben Kano zagaye na 2: Ku guji 'yan takara masu dabi'ar Jaki, Kare ko Kaza - Sheikh Kalil

Zaben Kano zagaye na 2: Ku guji 'yan takara masu dabi'ar Jaki, Kare ko Kaza - Sheikh Kalil

Wani shahararren malami kuma Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya ja kunnen al’umman jihar kan cewa ya zama dole su guji zaben duk wani dan takarar kujerar gwamna mai halayya irin na jaki, kare da kaza a zaben da za a sake gudanarwa a ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Shehin malamin ya ya yi wannan jan kunne ne yayinda yake zantawa da jaridar Leadership. Yace, a kullun idan mutum zai zabi shugaba toh ya duba nagartarsa, idan dai ya na da jajircewa da hangen nesa da kuma burin sama wa al’umma kyakykyawar makoma ta ilimi da sana’o’i da ayyuka da mutuncinsu da darajarsu.

Yace akwai bukatar neman zabi na mafi alkhairi da zabin Allah maimakon bin son rai ko kuma abunda mutum ke ki.

Zaben Kano: Wani shehin malami ya gargadi jama’a akan zabar wani dan takara
Zaben Kano: Wani shehin malami ya gargadi jama’a akan zabar wani dan takara
Asali: UGC

Sheikh Khalil yace, dabi’ar kare ita ce rashin mutunci, ta yadda duk wata nagarta kamar hakuri da juriya ta kare ya na da wata, illa wacce duk ta rusa wani abin yabo ga kare kamar yadda Turawa su ke yabon kare, domin idan ka dauke shi gadi, idan batagari sun zo su na kokarin samun ka duk haushin da ya ke yi idan ka jefa mi shi kashi ko ko kuli-kuli ko wani abu da ya ke so, to zai bar wannan haushin ya ci kayansa.

Yace: “To, akwai ’yan siyasa da duk rashin daidan abu, idan a ka jefa mu su wani abu da su ke so ko da wannan abin karya a ka yi mu su, sai ka ga sun yi ribas sun kuma kare karya da rashin mutunci. Dabi’ar kare kenan, ko guje su.

“Shi kuma jaki za ka ga sayen shi a ke yi da kudi, idan an saye shi an biya, to kaya a ke dora ma sa bai san kowane irin kaya ba ne; da kayan laifi da kayan litattafai duk bai sani ba. Shi dai an saye shi an biya, sai a yi ta dora ma sa kaya. Wannan shi ne dabi’ar jaki, ku guje shi.

KU KARANTA KUMA: Ban taba tsoma baki na cikin harkar zaben Gwamna Jihar Kano ba – Tinubu

“Sai dabi’ar kaza. Akwai ’yan siyasa masu dabi’ar kaza, wadanda su duk abinda ka ba su mai kyau sai sun je bola ko juji sun ci abinci, domin idan ka ba wa kaza tsabar gero ko dawa, to komai cin da ta yi sai ka gan ta a juji ta na cin datti da dai sauransu.

“Don haka mutane mu jajirce mu zabi shugaban da zai gina rayuwar al’umma, ba wanda zai zama koma-baya ba.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel