Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Tinubu da Bisi Akande (Hotuna)

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Tinubu da Bisi Akande (Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin manyan jigogin jam'iyyar All Progressives Congress APC, a ranar Talata, 19 ga watan Marism 2019 a fadar shugaban kasa dake Aso Villa, birnin tarayya, Abuja.

Mai magana da yawun shugaba Buhari, Femi Adesina, ya bayyana cewa Buhari ya karbi bakuncin jigon APC ta kasa kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, da tsohon shugaban jam'iyyar APC, Bisi Akande.

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Tinubu da Bisi Akande (Hotuna)
Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Tinubu da Bisi Akande (Hotuna)
Asali: Facebook

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta amince da mafi karancin albashin N30,000

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Tinubu da Bisi Akande (Hotuna)
Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Tinubu da Bisi Akande (Hotuna)
Asali: Facebook

Wannan ya biyo bayan ziyarar gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abubakar, a ranar Litinin inda ya kawowa shugaba Buhari karar hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, cewa ana shirin yi masa tuggu bayan hukumar tace an fasa gudanar da zabe zagaye na biyu a jihar.

Bayan ganawar, gwamnan ya bayyana cewa Buhari ya bashi shawara ya shigar da hukumar kotu kuma abinda zai yi kenan.

Hakazalika Buhari ya karbi bakuncin gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, domin sanar da shi yadda ake ciki kan zabe zagaye na biyu dai gudana a jihar ranar Asabar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel