Yakin sunkuru: Nakiyar 'yan Boko Haram ta kashe mutane 8 a Gwoza

Yakin sunkuru: Nakiyar 'yan Boko Haram ta kashe mutane 8 a Gwoza

Wasu nakiyoyi da ake kyautata zaton 'yan ta'addan Boko Haram ne suka dasa su sun yi sanadiyyar ajalin matafiya akalla mutane 8 a garin Gwoza dake zaman karamar hukuma a jihar Borno ta Arewa maso gabashin Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito lamarin ya faru ne a kauyen Warabe dake nisan kilomita 15 daga garin Gwoza, inda wata mota dake dauke da mutanen takwas ta bi ta kan bamabaman a cikin rashin sani, inda nan take bamabaman suka tashi motar, duka mutane 8 suka mutu.

Yakin sunkuru: Nakiyar 'yan Boko Haram ta kashe mutane 8 a Gwoza
Yakin sunkuru: Nakiyar 'yan Boko Haram ta kashe mutane 8 a Gwoza
Asali: UGC

KU KARANTA: Ana shirin tsige gwamnan Imo, Okorocha

Motar na cikin jerin ayarin motocin fararen hula ne wadanda Sojoji ke yi ma rakiya zuwa garin Pulka, amma sai direban motar ya sauka daga kan titi da nufin tsere ma motar dake gabansa, saukarsa daga hanya keda wuya ya bi ta kan bamabaman dake binne a gefen hanya.

Wani jami’in Soja ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace mayakan Boko Haram ne suka binne bamabaman da nufin jefa rayuwar mutanen karkara cikin hadari, kamar yadda suke yi a sauran kauyukan jahar Borno.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa wannan ba abin mamaki bane sakamakon yan ta’addan dake karkashin jagorancin Abubakar Shekau sun mamaye yankin, domin kuwa ko a watan data gabata sun jefa bom cikin Masallaci wanda ya kashe mutane uku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel