Da duminsa: Jonathan ya kira Gbenga Daniel, ya roke shi da ya tsaya a PDP

Da duminsa: Jonathan ya kira Gbenga Daniel, ya roke shi da ya tsaya a PDP

- Goodluck Jonathan ya jagoranci wasu shuwagabannin PDP, zuwa ga Otunba Gbenga Daniel, domin tausasa zuciyarsa da nufin canja ra'ayinsa na barin jam'iyyar

- A ranar Asabar ne Daniel ya sanar da ficewarsa daga PDP da kuma yin ritaya daga harkokin siyasa, yana mai cewa yana so ya dauki wata hanyar a rayuwarsa

- Sai dai har yanzu PDP ba ta fito fili ta yi tsokaci kan yin murabus din Daniel ba; sai dai hakan na iya faruwa a wani taron gaggawa da za ta gudanar a ranar Talata

Tsohon shugaban kasar Nigeria Goodluck Jonathan ya jagoranci wasu shuwagabannin PDP, inda suka yi kira ga Otunba Gbenga Daniel, tsohon gwamnan jihar Ogun, domin tausasa masa zuciyarsa tare da canja masa ra'ayi na barin jam'iyyar.

A ranar Asabar ne Daniel ya sanar da ficewarsa daga PDP da kuma yin ritaya daga harkokin siyasa, yana mai cewa yana so ya dauki wata hanyar a rayuwarsa, wanda ya hada da ci gaba da kula da gidauniyar tallafinsa mai suna GFF, da kuma farfado da cibiyar 'yan siyasar da suka yi ritaya daga harokin siyasa POLA, wacce aka gina shekarun baya da nufin ilimantar da jama'a kan harkokin siyasa.

Sai dai, manyan shuwagabannin PDP, da suka hada da Jonathan sun yi kira a gare shi da ya hakura ya zana a PDP ba sai ya koma APC ba.

KARANTA WANNAN: Tushen arziki: Yanzu Nigeria na fitar da tan 8m na shinkafa kowacce shekara - RIFAN

Da duminsa: Jonathan ya kira Gbenga Daniel, ya roke shi da ya tsaya a PDP
Da duminsa: Jonathan ya kira Gbenga Daniel, ya roke shi da ya tsaya a PDP
Asali: Twitter

Kamar yadda sanarwar ta gabata akan dalilin ficewarsa daga jam'iyyar, Legit.ng ta tattara rahoto kan cewa Daniel ya sanarwa Atiku Abubakar, wanda ya taba rike masa babban daraktan yakin zabensa, da kuma shi kansa Jonathan kafin ya fito fili ya bayyanawa jama'a matsayarsa.

Atiku ya ce abun zai zama da zafi idan aka ce ya bar jam'iyyar, yayin da Jonathan ya karfafi guiwarsa da ya sake nazari kan wannan mataki da ya dauka.

SaharaReporters ta tabbatar da cewa Daniel ya sanar da matsayarsa a ranar Asabar, inda Jonathan ya sake kiransa tare da danne zuciyarsa akan canja matsayarsa, yana mai cewa hjar yanzu PDP na bukatar 'yan siyasa irinsa.

Sai dai har yanzu PDP ba ta fito fili ta yi tsokaci kan yin murabus din Daniel ba; sai dai hakan na iya faruwa a wani taron gaggawa da kwamitin gudanarwar jam'iyyar na kasa ya shirya gudanarwa a ranar Talata.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel