Abun bakin ciki yayinda yar ajin karshe a jami’a ta mutu a hatsarin mota a Sokoto (katin shaida)

Abun bakin ciki yayinda yar ajin karshe a jami’a ta mutu a hatsarin mota a Sokoto (katin shaida)

Wani abun bakin ciki ya faru a karamar hukumar Dange Shuni da ke jihar Sokoto a ranar Lahadi, 17 ga watan Maris, inda wata matashiya yar ajin karshe a jami’a mai suna Munirah Adamu ta rasa ranta da misalin karfe 4:30pm a wani mumunan hatsari a hanyarta na dawowa daga makaranta a jihar Zamfara.

An wallafa labarin mumunan lamarin ne a nshafin Twitter na wani mai suna @Ibrahim_Bello inda ya wallafa labarin tare da katin shaidar marigayar.

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, babu tabbacin ko iyalan Munirah sun san da hatsarin da kuma mutuwarta.

KU KARANTA KUMA: Zaben Bauchi: Gwamna Abubakar ya ziyarci Aso Rock, ya gana da shugaba Buhari

Afkuwar hatsarurruka na daga cikin manyan kalubalen da gwamnatin Najeriya ke fuskanta. Yan makonni da suka gabata iyalan wata matashiyar yarinya mai suna Kemi Adeniran sun shiga halin bakin ciki biyo bayan mutuwarta.

Kemi Adeniran, wacce ta kamala karatu daga jami’ar Adekunle Ajasin, Akungba-Akoko (AAUA) ma ta gamu da ajalinta ne a wani hatsari da ya afku.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel