Kananan hukumomi 14 da za'a gudanar da zabe a Adamawa

Kananan hukumomi 14 da za'a gudanar da zabe a Adamawa

Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta bayyana adadin kananan hukumomin da za'a gudanar da zaben gwamna zagaye na biyu a jihar Adamawa ranar Asabar, 23 ga watan Maris, 2019.

Shugaban hukumar INEC na jihar Adamawa, Kasin Gaidam ya bayyanawa manema labarai ranar Lahadi a Yola cewa za'a gudanar da zaben ne a unguwanni 29, rumfunan zabe 44 inda akwai kuri'u 44,000.

Kananan hukumomin da za'a gudanar sune:

1.Yola ta kudu

2.Fufore

3. Ganye

4. Girei

5. Guyuk

6. Hong

7. Lamurde,

8. Numan,

9. Madagali,

10. Michika,

11. Mubi North,

12. Shelleng,

13. Song

14. Toungo

KU KARANTA: Hankalin jama'a ya tashi yayinda aka kashe kwamandan Soji a Bauchi

A jawabinsa yace: "Hukumar ta shiryawa zaben gwamna zagaye na biyu a jihar. Za'a gudanar da zaben ne a unguwanni 29, rumfunan zabe 44 inda aka share kuriu 44,000 a zaben da aka gudanar a baya."

"Duk Wani adadin da ke yawo bogi ne saboda rahoton da baturen zabe ya saki kadai ne na gaskiya."

Baturen zaben gwamnan jihar Adamawa, Farfesa Andrew Haruna, ya sanar da cewa dan takaran jam'yyar Peoples Democratic Party (PDP) candidate, Ahmadu Fintiri, ya samu kuri'u 367,472 yayinda dan takaran APC, Gwamna Jibrilla Bindow, ya samu kuri'u 334,995.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel