Kungiyar Izala reshen Jihar kano ta ba CP Wakili kyautar Kur'ani da littafan Musulunci

Kungiyar Izala reshen Jihar kano ta ba CP Wakili kyautar Kur'ani da littafan Musulunci

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, Muhammad Wakili ya ziyarci Shugaban kungiyar Izala na jihar, Dr. Abdullahi Saleh Pakistan a yau Asabar, 16 ga watan Maris.

Kwamishinan ya kai wannan ziyara ne domin girmamawa da kuma samun kwarin gwiwa a ayyukan da yake aiwatarwa a jihar Kano.

A yayin ziyayar, Dr. Abdullahi Saleh Pakistan ne ya fara gabatar da jawabai na nasiha da jan hankali ga CP Wakili akan ya rike aikinsa hannu biyu-biyu, kuma yasan cewa Allah zai tambayeshi akan dukkan abinda ya gabatar.

Kungiyar Izala reshen Jihar kano ta ba CP Wakili kyautar Kur'ani da littafan Musulunci
Kungiyar Izala reshen Jihar kano ta ba CP Wakili kyautar Kur'ani da littafan Musulunci
Asali: UGC

"Ka sani cewar dukkan aikin da mutum yake yi, zai iya wakiltar musulunci a wajen, ka yi iyaka kokarinka wajen kare musulinci da aikin da kakeyi. Kuma kayi Adalci a aikinka, domin Allah zai tsayar dakai yayi maka hisabi a kiyama," Inji Dr. Pakistan

Dr. Abdulmudallib Muhammad, shi ma ya dora da nasiha ga CP wakilin, duk dai don fita hakkin shari'a akansa.

Kungiyar Izala reshen Jihar kano ta ba CP Wakili kyautar Kur'ani da littafan Musulunci
Yayinda shugaban Izala ke gabatar da Kur'ani ga CP Wakili
Asali: UGC

Shi ma a nasa bangaren, CP Wakili ya ce ya ji dadin nasihun da Malaman suka gabatar masa, inda ya ce, dama yana bukatar nasiha domin ya samu kwarin gwiwa a inda yake yin daidai, ya kuma gyara inda yake da kusakurai.

''Ni ba na siyasa, ba ni da Jam'iyya, kuma ba zan siyar da lahira ta akan duniya ta ba, balle na siyar da lahirata akan duniyar wani, kun ga babbar asara kenan'', inji CP Waliki.

KU KARANTA KUMA: Zaben gwamna: Yan asalin jihar Kano mazauna Amurka da Turai sunce suna tare da Ganduje

Kungiyar Izala reshen Jihar kano ta ba CP Wakili kyautar Kur'ani da littafan Musulunci
Kungiyar Izala reshen Jihar kano ta ba CP Wakili kyautar Kur'ani da littafan Musulunci
Asali: UGC

CP Wakili ya bukaci malaman Kungiyar Izala, su taya shi addu'a domin dacewa a aikinsa, sannan ya bukaci a ko yaushe idan ya yi kuskure to a gyara masa.

A karshe, Dr. Pakistan ya gabatar da kyautar Alqur'ani mai girma, da littattafai na addinin musulunci da Kwamishinan ÿan sandan na Kano

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel