‘Dana ya nemi inyi masa addu’a kafin ya fita – Mahaifin wani yaro da ya mutu a rushewar gini

‘Dana ya nemi inyi masa addu’a kafin ya fita – Mahaifin wani yaro da ya mutu a rushewar gini

Wani abun bakin ciki ya afku a ranar 13 ga watan Maris, lokacin da wani ginin bene mai hawa uku ya ruguzo wanda a saman akwai makaranatr Firamare, gidaje da shagunan haya a Itafaji, birnin Lagas.

Lamarin yayi sanadiyar rasa rayuka da dama ciki harda na wasu daliban makarantar Firamare.

Mahaifin daya daga cikin daliban da abun ya shafa, Abdulfatah Ayoola, ya kasancee cikin wani hali bayan an tabbatar da mutuwar dansa mai shekaru shida, Fawaz.

An tattaro cewa an tono gawar Fawaz daga cikin rusasshen ginin da misalin karfe 2:00 na ranar da abun ya afku.

‘Dana ya nemi inyi masa addu’a kafin ya fita – Mahaifin wani yaro da ya mutu a rushewar gini
‘Dana ya nemi inyi masa addu’a kafin ya fita – Mahaifin wani yaro da ya mutu a rushewar gini
Asali: UGC

Da yake jawabi ga jaridar The Cable, Ayoola ya bayyana cewa ‘dansa ya nemi yayi masa addu’a kafin ya bar gida zuwa makaranta a wannan rana inda shi kuma ya aikata hakan, ba tare da sanin cewa haduwarsu ta karshe kenan da dan nasa ba.

KU ARANTA KUMA: Dino Melaye yace Buhari ya aro fiye da Dala Biliyan 40 a cikin shekaru 3

Mahaifin yaron yace: “Ya makara wajen zuwa makaranta a wannan rana. Bayan ya ci kalaci, sai ya nemi in bashi kudi amma sai na fada mashi cewa baya bukatar kudi tunda akwai abincin rana a tare da shi. Sai yace, ‘daddy, yi mun addu’a kafin na tafi’, sai nayi masa kamar yadda ya bukata. Sai ya tafi makaranta wanda babu nisa daga gida.”

Sai dai, mahaifin yaron wanda ya kasa rike hawayensa yayi bayanin cewa ba zai iya ja da ikon Allah ba sai dai yayi addu’a da kuma lallashin mahaifiyar yaron. Ya kara da cewa ya san wani da ya rasa yara hudu a annobar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel