Bayan zagayen zaben farko, mutan Kanon Dabo sun koma rayuwar kasuwancinsu

Bayan zagayen zaben farko, mutan Kanon Dabo sun koma rayuwar kasuwancinsu

Bayan haya-hayan siyasan da ya shafi rayuwar kasuwancin mutan Kanon Dabo a kwanakin nan, mutan jihar sun koma rayuwarsu ta yau da kullum cikin kwanciyar hankali bayan hukumar INEC ta zabi sabon rana domin kammala zaben gwamnan.

Jaridar Chronicle ta bada rahoton cewa kwana biyu bayan zaben gwamnan jihar Kabo, harkar kasuwanci ya dukufa musamman saboda tsoron barkewan rikici tsakanin mambobin jam'iyyun hamayya.

Hakazalika ranar Litinin, yan kasuwa da dama sun bude shaguna amma ba duka ba saboda ba'a gama sanar da sakamakon zaben ba.

Rahoton ya kara da cewa dukkan manyan kasuwannin cikin gari sun bude kuma sun cigaba da kasuwancinsu bayan hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta sanya ranan kammala zaben.

KU KARANTA: An sake tsintar wata gawa a cikin rijiya a jihar Filato

A kasuwar Singa, shugaban yan kasuwan, Alhaji Uba Zubairu Yakassai, ya bayyanawa manema labarai cewa rayuwa ta dawo daidai.

Yace: "Kasuwarmu ta cika yau kuma mun koma kasuwancinmu kamar yadda muka saba. Kana mun samu sabbin kwastamomin da suka shigo jihar domin sayayya."

A kasuwar Kantin Kwari, jama'a sun bude shagunansu. Wani mai sayar da atamfa, Muhammad Nasir Ali, ya bayyana cewa an koma kasuwa amma har yanzu kwastamomi daga wajen jihar.

Hakazalika a kasuwar Kurmi, mai sayar da littafai, Abdussalam Muhammad Yankaba, ya ce an bude kasuwa amma babu kasuwa kamar yadda aka saba.

A kasuwar kayan miya dake yan kaba kuwa, yan kasuwa sun bude kasuwancinsu kuma komai na tafiya dai-dai.

A kasuwar Sabon gari kuma, wani mai shagon magunguna, Mahmud Wapa, ya ce an daow kasuwa tun ranar Litinin amma jama'a basu fito sosai ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel