Tiryan-tiryan: Jerin rumfunan mazabun da za'a sake kada kuri'a a zaben gwamnan Kano

Tiryan-tiryan: Jerin rumfunan mazabun da za'a sake kada kuri'a a zaben gwamnan Kano

Bayan kammala tattara sakamakon zaben kananan hukumomi 44 na jihar Kano, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ta kaddamar da cewa sai an sake gudanar da zabe a mazabun wasu kananan hukumomi na jihar.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, babban Bature kuma Kwamishinan zabe na jihar Kano, Farfesa Riskuwa Shehu shine ya bayyana hakan a daren yau na Litinin cikin hedikwatar INEC da ke birnin Kanon Dabo.

Tiryan-tiryan: Jerin rumfunan mazabun da za'a sake kada kuri'a a zaben gwamnan Kano
Tiryan-tiryan: Jerin rumfunan mazabun da za'a sake kada kuri'a a zaben gwamnan Kano
Asali: UGC

KU KARANTA: Hukumar INEC ta sa akama jami'in ta a Imo

A cewar sa, dan takarar kujerar gwamnan jihar na jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, ya samu gamayyar kuri'u 1,014,474 yayin da dan takara na jam'iyyar APC, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya samu kuri'u 987,819.

Ga dai jerin Tiryan-tiryan: Jerin rumfunan mazabun da za'a sake kada kuri'a a zaben gwamnan:

Bichi: Rumfar zabe daya

Dawakin Kudu: Rumfar zabe daya

Doguwa: Rumfunan zabe 8

Gabasawa: Rumfunan zabe 5

Gezawa: Rumfar zabe 1

Sumaila: Rumfunan zabe 3

Warawa: Rumfunan zabe 3

Kiru: Rumfar zabe 1

Rimin Gado: Rumfar zabe 1

Wudil: Rumfar zabe 3

Tudun Wada: Rumfar zabe 4

Minjibir: Rumfar zabe 10

Rogo: Rumfar zabe 4

Kura: Rumfar zabe 1

Takai: Rumfar zabe 4

Kano Municipal: Rumfar zabe 4

Nassarawa: Ana tababar yawan rumfunan lokacin wannan rahoton

Dala: Ana tababar yawan rumfunan lokacin wannan rahoton

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel