Arewa na bukatar jagora irin Kwankwaso inji wani babban malami a Arewa

Arewa na bukatar jagora irin Kwankwaso inji wani babban malami a Arewa

An bayyana cewa, a halin da Arewa ta tsinci kanta a yanzu ta na bukatar jagororin da za a rika saurarar maganarsu kuma a yi aiki da ita kamar tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Rabiu Musa Kwankwaso.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin shugaban majalisar malamai ta kasa reshen jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, a zantawarsa da wakilinmu a Kano.

Arewa na bukatar jagora irin Kwankwaso inji wani babban malami a Arewa
Arewa na bukatar jagora irin Kwankwaso inji wani babban malami a Arewa
Asali: UGC

KU KARANTA: EFCC ta kama wani gwamnan APC da badakalar kudi

Sheikh Khalil ya kara da cewa, babbar matsalar da yankin ke fama da shi a Najeriya a halin yanzu shi ne rashin jagora guda daya wanda zai jagoranci al’umma zuwa ga tudun mun tsira, ya na mai danganta wannan matsala da karancin girmama na gaba.

Ya ce, duk wanda a ka kawo a ka ce a saka shi gaba a matsayin shi ne jagoran yankin wanda za a rika girmama umarninsa, sai ka ga an rufar ma sa da sara da suka na batanci, ya na mai cewa hatta wanda ya kawo sunan jagoran shi ma ba zai tsira daga sharrin magauta ba.

A cewar sa, sabanin yankin Yarabawa da ke Kudu maso Yamma, wadanda a koyaushe su ke yin biyayya ga jagoransu a kan alkibla guda daya tun daga kan Awolowo har zuwa Tinubu su 'yan Arewa ba haka suke ba.

A cewar shehin malamin, Arewa ma ta na da bukatar mutum irin Kwankwaso jajirtacce, mai gaskiya da amana, wanda ba ya yaudara kuma ya ke da cikakken tsarin da zai dore.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel