Magoya bayan APC da PDP sun tafka abun kunya a jihar Akwa Ibom

Magoya bayan APC da PDP sun tafka abun kunya a jihar Akwa Ibom

Akalla mutane takwas ne suka jikkata a yayin wani artabu a tsakanin magoya bayan manyan jam'iyyun Peoples Democratic Party (PDP) da kuma All Progressives Congress (APC) a mazaba ta 9 rumfa ta 007 a karamar hukumar nsit Atai, jihar Akwa Ibom.

Sai dai bayanan kuma rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu sun bayyana mana cewa mafiya yawan wadanda suka ji raunin a sakamakon fadan 'yan jam'iyyar APC kuma tuni har an kai su wata asibi mafi kusa domin karbar kulawar likita.

Magoya bayan APC da PDP sun tafka abun kunya a jihar Akwa Ibom
Magoya bayan APC da PDP sun tafka abun kunya a jihar Akwa Ibom
Asali: UGC

A wani labarin kuma, hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta cafke babban akawun gwamnatin jihar Imo, mai suna Uzo Casmir bisa zargin karkatar da kudin jihar.

Haka ma dai hukumar ta Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) tana zargin babban akawun da hade kai da gwamnan jihar ta Imo, Mista Rochas Okorocha wajen karkatar da kudin jahar da yakai Naira biliyan 1 da dubu hamsin don sayen kuri'u a zaben gwamna da 'yan majalisun jihar da za'a gudanar a ranar Asabar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel