2019: Ganduje ya sha kashi a hannun PDP a Unguwar Magwan

2019: Ganduje ya sha kashi a hannun PDP a Unguwar Magwan

Mun samu labari cewa kam’iyyar PDP mai adawa a jihar Kano ce ta lashe akwatin Unguwar Magwan inda nan ne mataimakin gwamnan jihar Kano watau Dr. Nasiru Yusuf Gawuna yake zabe.

‘Dan takarar PDP, Abba Kabir Yusuf, shi ne yayi nasara a rumfar zaben da ke Magwan da ke cikin Unguwar Gawuna a cikin karamar hukumar Nasarawa. Abba Yusuf ya lashe duka akwatuna 3 da ke cikin Magwan a zaben yau.

Daily Trust ta rahoto PDP ta samu kuri’a 210 ne a yankin yayin da APC mai mulki ta samu kuri’u 197. Har a akwatin da mai girma mataimakin gwamna yake yin zabe, ‘dan takarar PDP Abba Yusuf ya doke APC da kuri’a 3.

KU KARANTA: Jami'an tsaro damke mota da kayan zabe a Yankin Mataimakin Ganduje

2019: Ganduje ya sha kashi a hannun PDP a Unguwar Magwan
Surukin Kwankwaso Abba Yusuf ya doke APC a Gawuna
Asali: Twitter

Jaridar tace jam’iyyar PDP ta samu kuri’a 76 inda APC kuma ta tashi da 73 a rumfar Nasiru Gawuna da ke cikin Magwan. A sauran akwatun yankin, PDP mai adawa ta samu 63 da 76 yayin da APC ta iya samun kuri’u 48 da kuma 71.

A yau dinne kuma aka damke wata mota cike makil da kayan zabe a wata makaranta da ke cikin Magwan din inda nan ne Yankin da Mataimakin Gwamnan jihar Kano Nasiru Gawuna mai-ci ya fito.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel