Zaben gwamnoni: Jahohin Arewa da jam'iyyar APC za ta iya lashewa

Zaben gwamnoni: Jahohin Arewa da jam'iyyar APC za ta iya lashewa

Katsina: Yanzu haka dai APC ce ke da iko a jihar, kuma ana sa ran Gwamnan jihar zai sake lashe zaben sa

Jigawa: Kamar Katsina, ita ma jihar Jigawa ana ganinncewa jam'iyyar APC da ke mulki a jihar ba za ta sha wata wahala ba wajen lashe zaben na gwamna.

Zaben gwamnoni: Jahohin Arewa da jam'iyyar PDP za ta iya lashewa
Zaben gwamnoni: Jahohin Arewa da jam'iyyar PDP za ta iya lashewa
Asali: Depositphotos

Zamfara: Duk da dai da farko an yi ta takadda game da 'yan takarar APC a jihar, amma daga baya APC din ta samu damar shiga zaben kuma har ma ta lashe dukkan zababbun kujerun 'yan majalisar tarayya. Ana ganin APC zata iya sake lashe zaben gwamna

Kebbi: Masu sharhin harkokin kwallo dai na ganin jihar ta Kebbi kusan ba jam'iyyun adawa ma. Don haka APC na da kyakkyawan zaton zata lashe zaben gwamna.

Borno: Duba da irin yawan kuri'un da APC ta samu zaben shugaban kasa a Borno, ana ganin zaben gwamna ma zai iya zuwa hakan.

Yobe: Ita ma dai Yobe ana ganin APC ce zata lashe zaben jihar musamman ma ganin cewa PDP dake zaman babbar jam'iyyar adawar kasar bata taba mulkar jihar ba.

Kwara: Sakamakon da PDP ta samu a zaben shugaban kasa da kuma faduwar zaben da Sanata Bukola Saraki yayi a zaben da ya gabata, ana ganin dai cewa tamkar 'yar manuniya ce akan abun da zai iya faruwa a zaben gwamna.

Neja: Duk da jam'iyyar PDP na da karfi a jihar ta Neja, amma dai ana ganin cewa APC tafi karfi da farin jini a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel