Keyamo ya mayar wa da Obasanjo martani, ya fadi waye maigidan Buhari na gaske

Keyamo ya mayar wa da Obasanjo martani, ya fadi waye maigidan Buhari na gaske

- Festus Keyamo, babban lauyan Najeriya ya mayar da martani ga tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo akan Buhari

- Keyamo yace babban ubangidan kowa a Najeriya shine Yakubu Gowon

- Hakan martani ne ga furucin da Obasanjo yayi na cewa shi ubangidan shugaban kasa Buhari ne don ya fi shi dadewa a mulki

Festus Keyamo, babban lauyan Najeriya kuma kakakin kungiyar kamfen din Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya mayar da martani ga tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo inda yake cewa zai ci gaba da sukar Buhari saboda shi Ubangidansa ne sannan cewa ya rike matsayin Shugaban kasa fiye da kowa.

Obasanjo yayi wannan furucin ne yayinda yake bikin cikarsa shekaru 82 a duniya a ranar Talata, 5 ga watan Maris a Abeokuta, babbar birnin jihar Ogun.

Keyamo ya mayar wa da Obasanjo martani, ya fadi waye maigidan Buhari na gaske
Keyamo ya mayar wa da Obasanjo martani, ya fadi waye maigidan Buhari na gaske
Asali: Depositphotos

Don haka da yake martani ga wannan furuci na tsohon Shugaban kasar a ranar Laraba 6 ga watan Maris, Keyamo ya nuna rashin amincewarsa kan haka, inda ya ce Yakubu Gowon ne ya riki matsayin na tsawon lokaci amma ba Obasanjo ba.

Keyamo ya rubuta: “Kai tsaye ba tare da kwana-kwana ba: Ubangidan kowa a Najeriya a yau shine Janar Yakubu Gowon wanda ya yi mulkin soja mafi tsawo . shine babban kowa. Kuma duk sanda ka ga ya je Villa toh ya je bayar da shawara mai amfani ne.”

KU KARANTA KUMA: Fara wa da iya wa: Atiku ya samu nasara ta farko a kotun sauraron karar zabe

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa kalubalantar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ke yi ba wai domin kiyayya bane. Ya ce yana kalubalantar gwamnati Buhari saboda har yau har gobe shi ubangidan shugaban kasar ne.

A cewar Obasanjo, "Ina kalubalantar shirye shirye da tsare tsare na gwamnati mai ci a yanzu domin tabbatar da cewa abubuwa na tafiya yadda ya kamata bisa tsari na demokaradiyya."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel