Yanzu Yanzu: Ameachi ya goya wa dan takaran jam’iyyar AAC baya a Rivers

Yanzu Yanzu: Ameachi ya goya wa dan takaran jam’iyyar AAC baya a Rivers

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Rivers da kuma yankin Kudu maso kudu, Rotimi Ameachi ya bayyana goyon bayansa ga dan takaran gwamna a jam’iyyan African Action Congress (AAC), Awara Biokpomabe.

Biyo bayan wannan lamarin, Ameachi ya bukaci mambobin APC da magoya bayanta a Rivers da su zabi Biokpomabo a ranar Asabar, wanda yakasance dan asalin Kula-kalabari a karamar hukumar Akuku-Toru dake jihar.

Ministan sufurin ya bayyana hakan ne a safiyar ranar Laraba, 6 ga watan Maris a Eleme, karamar hukumar Eleme dake jihar Rivers, yayin da yake gabatar da jawabi ga mambobin APC da magoya bayanta, gabannin zabe da za a gudanar a ranar 9 ga watar Maris.

Yanzu Yanzu: Ameachi ya goya wa dan takaran jam’iyyar AAC baya a Rivers
Yanzu Yanzu: Ameachi ya goya wa dan takaran jam’iyyar AAC baya a Rivers
Asali: Depositphotos

Ya bayyana cewa ko da yake babbar jam’iyyar adawa a jihar Rivers wato APC na a kotu bisa rashin sanya sunan dan takaranta, fasto Tonye Cole, haifaffan Abonnema-Klabari a karamar hukumar Akuku-Toru a takardar zabe.

KU KARANTA KUMA: Zan zage damtsen aiki sosai a wannan karon - Buhari

Ameachi ya karfafa cewa ya zama dole a goyi bayan dan takaran jam’iyyar AAC, ganin kusancin zaben gwamnoni da na majalisar jiha.

Ministan sufurin har ila yau ya bukaci mutanen Rivers da su fito kwansu da kwarkwatansu don zabar dan takaran jam’iyyar AAC, ya karfafa cewa akwai amfani da dama da zasu mora daga gwamnatin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel