Yan takarar gwamna 9 sun janye daga tseren a Adamawa

Yan takarar gwamna 9 sun janye daga tseren a Adamawa

Yan takaran gwamna tara a jihar Adamawa, sun janye daga tseren don mara wa dan takaran jam’iyyar PDP, Ahmad Umar Fintiri baya. A cewarsu sun yanke shawarar ne bayan samun goyon bayan mutanen jihar.

An tattaro cewa akwai hadin kai dake tasowa a jihar Adamawa gabannin zaben gwamnoni da za a gudanar a ranar Asabar, 9 ga watan Fabrairu.

Yan takara guda tara ne suka janye daga takaran, sun kuma mara wa dan takaran jam’iyyar PDP baya. Sun jaddada cewa Fintiri ne zai magance matsalolin da suke fuskanta wadanda suka shafi rashin hanyoyi, rashin cibiyoyi da rashin inganci a fannin ilimi.

Yan takarar gwamna 9 sun janye daga tseren a Adamawa
Yan takarar gwamna 9 sun janye daga tseren a Adamawa
Asali: UGC

Fintiri yayi murna da godiya ga yan takaran bisa karamcin da suka nuna mishi, ya basu tabbacin samun hadin kai a gwamnatinsa har idan aka zabe shi.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun tarwatsa gangamin kamfen din APC a Akwa-ibom

A baya Legit.ng ta rahoto cewa yayin da ake shirin zaben sabon gwamnan jihar Gombe, jam’iyyu 45 ne aka ji sun marawa Alhaji Inuwa Yahaya na jam’iyyar APC mai adawa a jihar baya domin ganin ya samu nasara.

Wadannan jam’iyyu da-dama, sun bayyana cewa Inuwa Yahaya, wanda ya tsaya a karkashin jam’iyyar APC, ya fi dukkan su cancanta da ya rike jihar.’Yan takarar su kace wannan ya sa su ka dauki matakin mara masa baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel