Dan Sule Lamido na shirin garzayawa kotu kan sakamakon zabe

Dan Sule Lamido na shirin garzayawa kotu kan sakamakon zabe

- Dan tsohon gwamnan jihar Jigawa, Mustapha Sule ya yanke shawarar shiga kotu akan sakamakon zabe

- Lamido dai ya nemi kujerar dan majalisar dattawa mai wakiltan yankin Jigawa ta tsakiya

- Sai dai Lamido ya sha kaye a hannun Sanata Sabo Nakudu

Dan tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma dan takarar kujerar sanata a yankin Jigawa ta tsakiya a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Mustapha Sule Lamido ya sanar da shitinsa na kalubalantar sakamakon zaben majalisar dokoki da ya gudana a ranar 23 ga watan Fabrairu a kotu.

Mataimakin Shugaban PDP a yankin Jigawa ta tsakiya, Aminu Jahun ya bayyana hakan ga manema labarai, cewa za su kalubalanci sakamakon zaben akan zargin magudi da aka tafka a zaben majalisar dokokin kasa a jihar.

Dan Sule Lamido ya garzaya kotu kan sakamakon zabe
Dan Sule Lamido ya garzaya kotu kan sakamakon zabe
Asali: UGC

Ku tuna cewa Sanata Sabo Nakudu ya kayar da dan tsohon gwamnan bayan ya samu kuri’u 224,543 inda shi kuma dan Lamido ya samu kuri’u 143, 611.

KU KARANTA KUMA: Dan asalin jihar Bauchi ya mutu yan kwanaki kadan bayan yayi wanka da shan ruwan kwata don murnar nasarar Buhari

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa gamayyar kungiyar Coalition of United Political Parties (CUPP) ta zargi hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) da tursasa mataimakin daraktan kungiyar yakin neman zaben dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), da ya mika shaidar da Atiku Abubakar yake yunkurin yin amfani da su a kotu.

Atiku ya kaddamar da lauyoyi yan kwanaki da suka gabata don kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranan 23 ga watan Fabrairu inda hukumar INEC ta bayyana dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel