Zan koma Daura da zama bayan na kammala mulkina na biyu - Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin komawa Daura, bayan kammala mulkinsa na biyu. Buhari yace zai koma da zama a gidansa da zaran y agama mulkinsa.
Ya bayyana akan ne a lokacin da ya karbi bakuncin sarakunan gargajiya karkashin jagorancin Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.
Ya bukaci sarakunan gargajiya da su yi yaki da laifuka, sannan Shugaban kasar ya bayyana cewa su shirya taka muhimmin rawa wajen hana ayyukan laifi a yankunansu.

Asali: Twitter
Shugaban kasar ya lissafa matakan da gwamnatinsa ta dauka domin inganta tsaron kasar yayinda ya mayar da hankali wajen tabbatar da daidaituwar al’amuran kasar.
KU KARANTA KUMA: Obasanjo ya yi magana kan abunda ke tsakaninsa da Buhari bayan zaben Shugaban kasa
A baya Legit.ng ta rahoto cewa kungiyar sarakunan gargajiya Najeriya a ranan Talata sun kaiwa shugaba Muhammadu Buhari ziyarar taya murna kan nasararsa akan zaben shugaban kasa.
Shugaban kungiyar kuma mai alfarma sarkin Musulmi, Saad Abubakar na uku, ya bayyana ra'ayinsa inda yace nasarar Buhari kaddara ce kawai daga Allah kuma kada wanda ya kalubalanci haka.
Yace: "Nasararka a zaben shugaban kasa karo na biyu a daukeshi a matsayinn abinda Allah ya kaddara kuma babu wani ma'alukin da zai iya canza kaddara."
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng