Kishin-kishin: Jaruma Nafisa Abdullahi ta kusa zama amarya

Kishin-kishin: Jaruma Nafisa Abdullahi ta kusa zama amarya

A cigaba da kawo maku labaran masana'antar shirya fina-finai ta Hausa wata Kanny wood, yau mun leko maku wani labari da ke ta yawo a masana'antar na cewa daya daga cikin fitattun fuskokin ta watau jaruma Nafisa Abdullahi na daf da zama amarya.

Wannan kishin-kishin din dai ta soma ne tun daga lokacin da jarumar ta je a shafin ta na dandalin sadarwar zamani na Tuwita ta rubata cewa "Yanzu ta tabbata" da turanci watau "It's official" sannan kuma ta sa alamar zobe.

Kishin-kishin: Jaruma Nafisa Abdullahi ta kusa zama amarya
Kishin-kishin: Jaruma Nafisa Abdullahi ta kusa zama amarya
Asali: UGC

KU KARANTA: Mai da'awar annabtar da yayi hasashen faduwar Buhari ya sake magana

Wannan dai kamar yadda muka samu, ya haifar da doguwar muhawara a shafin na ta inda mutane masu bibiyar ta suka yi ta yi mata Allah ya sa alheri da sauran addu'oi dai irin na masoya.

Sai dai kuma dukka a cikin muhawarar da aka tafka a kasar rubutun nata ciki kuwa hadda masu tambayar ta karin haske ko gaskiyar abun da ta rubuta, jarumar bata ba kowa ansa ba. Bata ce e da gaske ne ba ba kuma ta ce ba gaskiya bane ba.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya jarumar ta yi soyayya mai karfi da jarumi Adam Zango da har ma aka rika tunanin za suyi aure amma sai suka bata daga baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel