Dan Osama Bn Laden ya fallasa sirrin da ya sa duniya a rudani game da mahaifin sa

Dan Osama Bn Laden ya fallasa sirrin da ya sa duniya a rudani game da mahaifin sa

Daya daga cikin'ya'yan Osama Bin Laden, mai suna Hamza ya ce mahaifin sa yana nan da ran sa kuma ma shi kadai ya san ida gwamnatin Amurka ta boye mahaifin sa shine ma yasa shugabannin kasar ke ci gaba da farautar sa domin suga karshen sa.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa kasar ta Amurka a 'yan kwanakin nan ta sa kazar karfi akan dukkan wanda ya taimaka masu da muhimman bayanai akan neman da suke yi wa dan shugaban Al-Qaida, Osama bin Laden.

Dan Osama Bn Laden ya fallasa sirrin da ya sa duniya a rudani game da mahaifin sa
Dan Osama Bn Laden ya fallasa sirrin da ya sa duniya a rudani game da mahaifin sa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Malamin addinin da yayi hasashen faduwar Buhari ya sake wata magana

Legit.ng Hausa dai ta samu cewa kasar ta Amurka ta dauki alkawarin bai wa duk wanda ya bada cikakkun bayanai game inda yake,zunzurutun kudi dala milyan 1,000,000.

A cewar gwamnatin Washington, dan na shugaban Al Qaida, Hamza bin Laden ya wallafa wasu sakwanni da kuma bidiyo a shafinsa na Intanet, inda ya kira magoyansa da babbar murya da su hade wa Amurkawa kai.

Sai dai a nasa martanin, Hamza Bn Laden ya karyata da wannan batun, inda ya daga karshe ya ce Amurka ta dau alwashin kama shi ne saboda ya san inda gwamnatin Washington ta boye baban sa.

"Lafiyar mahaifina kalau ta ke. Shekaru biyu kenan da muke ganawa ta Watsapp.Ba shi wata matsala." A cewar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel