Boko Haram: Na kasa zuwa garinmu na tsawon shekaru hudu - Ali Modu Sherrif

Boko Haram: Na kasa zuwa garinmu na tsawon shekaru hudu - Ali Modu Sherrif

Tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff ya bayyana cewa tsawon shekau hudu ya kasa zuwa garinsa na karamar hukumar Ngala saboda rikicin Boko Haram.

Sherrif wanda ya kasace gwamnan jihar Borno tsakanin shekarar 2003 zuwa 2011 ya bayyanawa manema labaran fadar shugaban kasa hakan ne yayinda ya kaiwa shugaa Muhammadu Buhari gaisuwan taya murnan nasarar zabe.

Yace:" Idan ka duba tarihin dukkan wadanda sukayi takarar zabe da shugaba Buhari, babu wanda ke da kashi 1 bisa goman gaskiyarsa. Wannan shine mutum wanda ba da kwadayin abinda yan Najeriya ke kwadayi, satan kudi domin azurta kansu."

"Yana nan ne domin yan Najeriya, ya nada imanin cewa Najeriya zata cigaba. Jawabin yakin neman zabensa mai sauki ne, mun fara yaki da rashawa, habaka tattalin arziki da kuma kara ingancin rayuwar yan Najeriya."

"Wannan abu ya baiwa yan Najeriya sha'awa, misali, ban je kauyena ba na tsawon shekaru hudu kafin zaben 2015. Boko Haram sun kwace dukkan kananan hukumominmu a Borno, amma a yau, za ka iya zuwa ko ina a Borno."

Saboda haka duk abinda mutanen Borno suka yiwa shugaba Buhari ranar Asabar, kawai muna godiya ne kan abubuwan da yayi."

Mun kawo muku rahoton cewa tsohon gwamnan jihar Borno, Modu Sherrif, ya kaiwa shugaba Buhari ziyara ranar Juma'a kan nasarar da ya samu a zaban bana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel