Yanzu-yanzu: Mun mikawa Buhari bukatun Atiku - Janar AbdusSalam

Yanzu-yanzu: Mun mikawa Buhari bukatun Atiku - Janar AbdusSalam

Shugaban kwamitin zaman lafiya, AbdusSalam Abubakar, ya bayyana cewa kungiyarsa ta mikawa shugaba Muhammadu Buhari bukatun dan takaran shugaban kasa karkashin PDP, Atiku Abubakar kan sulhun da ake shiryawa.

Janar Abdusalam wanda ya gana da Atiku Abubakar ranan Talata, ya bayyana cewa wasu mambobin kwamitinsa sun gana da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa, Abuja.

Atiku wanda ya nuna rashin amincewarsa da sakamakon zaben da hukumar INEC ta sanar cewa shugaba Buhari ya lashe zabe kuma ya lashi takobin cewa zai garzaya kotu.

Abdusalam Abubakar tare da Bishop Mattew Kukah da John Onaiyekan sun shiga ganawa da shugaba Buhari ne misalin karfe 3 zuwa 4 na rana.

Wadanda ke halarce a ganawar sune shugaba jam'iyyar APC, Adams Oshiomole, da wasu masu ruwa da tsakin jam'iyyar.

KU KARANTA: Bayan maganar sallamar ministoci, Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron FEC na musamman

Mun kawo muku cewa Atiku Abubakar ya gabbatar da wasu muhimman bukatu 5 da ya ke so daga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Ga dai bukatun da ya gabatar kamar yadda aka ruwaito.

1. A bude dukkan asusun ajiyar banki na 'yan jam'iyyar hamayya da aka rufe

2. A dena tura sojoji wuraren zaben da za a gudanar a nan gaba

3. A rika tantance masu zabe kafin a fara kada kuri'u a sauran zabukan da su kayi saura

DUBA WANNAN: Yadda Buhari ya yi murdiyya wajen lashe zaben 2019 - Sheikh Ahmad Gumi

4. INEC ta bude shafinta na Intanet ta yadda dukkan jam'iyyun siyasar da ke takara za su iya shiga su duba yadda abubuwa ke gudana

5. A saki dukkan 'yan siyasar da ake tsare da su ba bisa kan ka'ida ba

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel