Wata-sabuwa: An yi zina da ma'aikatan mu lokacin zaben shugaban kasa - INEC

Wata-sabuwa: An yi zina da ma'aikatan mu lokacin zaben shugaban kasa - INEC

Hukumar shirya zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commisslon (INEC) ta bada labarin cewa an yi zina da wasu ma'aikatan ta mata a yayin zabukan da aka gudanar satin da ya gabata na shugaban kasa da 'yan majalisar wakilai.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da babban jami'in yada labarai da wayar da kan masu zabe na hukumar Mista Festus Okoye ya fitar dauke da sa hannun sa.

Wata-sabuwa: An yi zina da ma'aikatan mu lokacin zaben shugaban kasa - INEC
Wata-sabuwa: An yi zina da ma'aikatan mu lokacin zaben shugaban kasa - INEC
Asali: UGC

KU KARANTA: Dan takarar gwamna ya fatattaki 'yan gudun hijira a gidan shi

A cikin sanarwar, Mista Festus Okoye ya bayyana cewa duk da dai zaben da aka gudanar a iya cewa an yi shi ne cikin lumana a dukkan fadin kasar, amma dai hukumar ta dan samu tsaiko a wasu wuraren yayin zaben.

Ya ciga da cewa hukumar ta Independent National Electoral Commisslon (INEC) ta samu labarin tashe-tashen hankula da satar mutane da yiwa jami'an su fyade da ma rasa rai a wasu wuraren.

Haka zalika Mista Festus ya kuma yi anfani da damar wajen jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukan su ko jikkata koma rasa dukiya a wasu wuraren tare da basu hakuri da kuma tabbacin karin matakan tsaro daga hukumar domin kaucewa kara aukuwar lamarin a gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng