Zaben 2019: Buhari ya yiwa Atiku tazarar gaske a jihar Yobe

Zaben 2019: Buhari ya yiwa Atiku tazarar gaske a jihar Yobe

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa Atiku Abubakar gagarumar tazara ta gaske a yayin da sakamakon zaben kananan hukumomi biyar na jihar Yobe ya bayyana.

A yayin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta fidda sakamakon zaben kananan hukumomi biyar na jihar Yobe, mun samu cewa dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari, ya yiwa Atiku fintinkau, dan takara na jam'iyyar PDP.

Zaben 2019: Buhari ya yiwa Atiku tazarar gaske a jihar Yobe
Zaben 2019: Buhari ya yiwa Atiku tazarar gaske a jihar Yobe
Asali: UGC

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Farfesa Abubakar Gundiri, babban alkalin zabe na jihar Yobe ba ya ga kasancewar sa shugaban jami'ar Wukari, shine ya bayar da shaidar hakan a cibiyar kidaya da tantance kuri'u da ke birnin Damaturu.

Farfesa Gundiri ya ce Buhari ya lashe kuri'u 12,227 yayin da Atiku ya samu kuri'u 325 kacal a karamar hukumar Gujba. Yayin da Atiku ya samu kuri'u 1,269, Buhari kuma ya lashe kuri'u 12,122 a karamar hukumar Tarmuwa.

KARANTA KUMA: Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno

A karamar hukumar Damaturu, shugaban kasa Buhari ya lashe kuri'u 35,772 yayin da tsohon mataimakin shugaban kasa ya samu kuri'u 2,099. Yayin da Buhari ya samu kuri'u 22,377 a karamar hukumar Karasuwa, Atiku ya lashe kuri'u 3,692.

A yayin da ake ci gaba da kirdadon sakamakon sauran kananan hukumomi kasancewar jihar Yobe mai kunshe da kananan hukumomi 17, shugaban kasa Buhari ya yi galaba da kuri'u 14,619 a karamar hukumar Machina inda Atiku ya tashi da kuri'u 2,315 kacal.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel