Da duminsa: Orji Uzor Kalu ya lashe zaben sanatan Abia ta Arewa

Da duminsa: Orji Uzor Kalu ya lashe zaben sanatan Abia ta Arewa

Wani tsohon gwamnan jihar Abia kuma sanata mai ci a mazabar Abia ta Arewa karkashin jam'iyyar APC, Dr Orji Uzor Kalu ya samu nasarar lashe zaben sanatan Abia ta Arewa, a zaben ranar Asabar 16 ga watan Fabreru da aka kammala.

Rahotanni sun bayyana cewa Kalu ya samu nasara da kuri'u 30,580 yayin da abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Sanata Mao Ohuabunwa ya samu kuri'u 21,940.

Bisa kididdigar sakamakon zaben da aka sanar na kananan hukumo 5, APC ta samu kuri'u 8317 a karamar hukumar Isuikwuato yayin da PDP ta samu kuri'u 4,609.

KARANTA WANNAN: Daga gwamna zuwa majalisar dattijai: Amosun ya lashe zaben mazabar Ogun ta tsakiya

Da duminsa: Orji Uzor Kalu ya lashe zaben sanatan Abia ta Arewa
Da duminsa: Orji Uzor Kalu ya lashe zaben sanatan Abia ta Arewa
Asali: UGC

A karamar hukumar Ohafia kuwa, APC ta samu kuri'u 5521, yayin da PDP ta samu kuri'u 4861.

Bangaren karamar hukumar Bende kuwa, Mr Kalu ya samu kuri'u 10,701 yayin da abokin hamayyarsa, Mr Ohuabunwa, ya samu kuri'u 4,875.

Haka zalika, APC ta lashe zabe a karamar hukumar Arochukwu da kuri'u 1166 yayin da PDP ta samu kuri'u 843.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel