Sakamakon zaben Shugaban Kasa da ‘Yan Majalisun Tarayya a Jihar Kano

Sakamakon zaben Shugaban Kasa da ‘Yan Majalisun Tarayya a Jihar Kano

Sakamakon zabe ya fara fitowa daga wasu sassa na Jihar Kano kamar yadda mu ke samun labari. A cikin birnin Kano, mun ji cewa PDP ta rasa akwati mai lamba 021 na mazabar Sharada da ke cikin karamar hukumar Birni.

Sakamakon da mu ka ji shi ne APC ta lashe akwatin shugaban kasa da kuri'a 154, yayin da PDP ta samu 26. A kujerar Sanata kuma, PDP ta samu kuri'a 53 inda APC kuma ta tashi da 137. Har yanzu dai ba mu da tabbacin wannan labari.

A kujerar 'dan majalisar wakilai na tarayya kuma, jam'iyyar PDP ta iya samun kuri'u 34 rak. Yanzu haka dai Honarabul Dr. Abubakar Nuhu Danburam ne wanda yake rike da kujerar 'dan majalisar tarayya na yankin cikin Birnin na Kano.

KU KARANTA: 2019: Sakamakon zabe daga jihohin Bauchi, Gombe da Filato

Kamar yadda labari ya zo mana dakunan APC, a akwati na 28 na gundumar Sheka a cikin karamar hukumar na birni, APC ta samu kuri'a a 1551 a zaben shugaban kasa inda Atiku Abubakar na PDP ya samu kuri'a 162 tal.

Bayan karfe 2:00 na rana ne mu ka ji cewa Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje yan kan layin zabe inda yake jira a tantance sa domin ya kada kuri'ar sa a zaben shugaban kasa da kuma na 'yan majalisar tarayya da ake yi yau.

Ba da dadewa bane labari mu ka ji tsohon Gwamnan jihar Kano watau Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya isa filin zaben sa kuma har ya dangwala kuri'ar sa ya jefa takardar cikin akwatin zabe. Kwankwaso yana cikin manyan PDP.

Ana zaben Shugaban Kasa da ‘Yan Majalisun Tarayya a Jihar Kano

Tsohon Gwamna Kwankwaso yayi zabe a Jihar Kano
Source: Facebook

Kwankwaso ba ya neman wata kujera a zaben 2019 inda ya sallama mukamin sa na Sanata ga Honarabul Aliyu Madakin Gini wanda zai yi takara a PDP. Aliyu Gini zai kara ne da Ibrahim Shekarau a cikin jam'iyyar APC.

Da kimanin lokacin sallar azahar ne mu ka ji cewa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya kada kuri'ar sa a Jihar Kano. Sarki Sanusi II wanda shi ne tsohon gwamnan babban bankin Najeriya yayi na sa zaben ne a cikin Birnin Kano.

Bayan Mai Martaba Sarki Sanusi II, mun samu labari cewa 'Dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar PRP watau Salihu Takai ya kada kuri'ar sa a zaben shugaban kasa. Salihu Takai ya zabi Muhammadu Buhari ne kamar yadda mu ka ji.

KU KARANTA: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato

Ana zaben Shugaban Kasa da ‘Yan Majalisun Tarayya a Jihar Kano

'Dan takarar PDP na Gwamna a Jihar Kano ya kada kuri'ar sa
Source: Twitter

Shi ma dai 'dan takarar Gwamnan Kano a jam'iyyar PDP, Injiniya Abba Kabiru Yusuf ya kada na sa kuri'ar a cikin Jihar Kano. Abba Kabiru Yusuf yana samun goyon baya ne daga wajen tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso.

Mu na samun labari cewa ana sayen kuri'ar Talakawa yayin da ake kan layi na kada kuri'a a zaben shugaban kasa da kuma 'yan majalisar tarayya a jihar Kano. Kano ce inda APC ta fi samun kuri'a a zaben da aka yi a shekarar 2015.

Jaridar The Cable ta bada rahoto cewa ana biyan mutane kudi domin su zabi jam'iyyar da ake so a yankin Mandawari da ke cikin karamar hukumar Gwale. Kamar yadda mu ka ji ana raba N500 ne ga masu shirin kada kuri'a.

Mun kuma ji labari cewa rikici ya barke tsakanin jama'a da kuma Ma'aikatan tsaro a akwatin zaben da ke cikin wata makarantar sakandare da ke cikin Gwale a jihar ta Kano. A wasu wuraren kuma na'rurorin aikin zaben ba su aiki.

Ana shirin fara zaben Shugaban kasa da Majalisa a Jihar Kano

Tun cikin tsakar dare aka fara hawa layin zabe a Kano
Source: UGC

Wasu masu lura da aikin zaben 2019 a Najeriya sun bayyana cewa na'urar da ake amfani da su wajen tantance masu kada kuri'a sun gaza aiki a cikin Garin Madobi. Wannan ya sa aka yi watsi da na'urorin a Yankin Kanwa da ke cikin Madobi.

Kamar yadda labari ya zo mana, Matan aure da jama’a sun soma ajiye layi ne tun kusan karfe 2:00 na dare a cikin karamar hukumar Gwarzo da ke cikin yankin Arewacin jihar Kano, su na jiran ma’aikatan zabe su karaso cikin safiya.

KU KARANTA: Ana zaben 2019, Garin Gaidan a jihar Yobe ya fada hannun Boko Haram

Haka zalika kuma mun samu labari cewa da sanyin safiya Ma'aikatan zabe sun fara shirin gudanar da aikin zabe a Yankin Bunkure da ke cikin Jihar ta Kano. Jami’an zabe sun shigo yankin ne dai tun karfe 7:00 domin su karbi kayan aiki.

Bayan nan kuma mun ji cewa ana shirin fara zabe a cikin yankin Ginsawa da ke karamar hukumar Tofa. A akwatin zabe na 004 da ke cikin mazabar na Ginsawa, tun sa’a guda da ta wuce aka fara niyyar gabatar da zaben na shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel