Girman-ka-akwatin-ka: Jerin sunayen wasu manyan 'yan siyasa da suka fadi rumfar zaben su

Girman-ka-akwatin-ka: Jerin sunayen wasu manyan 'yan siyasa da suka fadi rumfar zaben su

Sakamon zabuka ke cigaba da kwararowa musamman ma a kafafen sadarwar zamani da kuma sauran kafafen yada labarai wadanda ba hukuma ba tun bayan zabukan da aka gudanar a dukkan fadin kasar ranar Asabar din da ta gabata.

Sai dai kamar yadda ake fada cewa a siyasance kowane dan siyasa bai da abun da zai yi tutiya da shi da ya wuce irin goyon bayan da yake da shi a rumfar zaben sa kasantuwar wannan ne ma'aunin sa na farko na karbuwa ko akasin haka a al'ummar sa.

Girman-ka-akwatin-ka: Jerin sunayen wasu manyan 'yan siyasa da suka fadi rumfar zaben su

Girman-ka-akwatin-ka: Jerin sunayen wasu manyan 'yan siyasa da suka fadi rumfar zaben su
Source: Original

Legit.ng ta tattaro mana wasu sakamakonnin da muka samu daga majiyoyin da ba na hukumar zabe ba amma muka tabbatar da sahihancin su na wasu fitattun 'yan siyasar da jam'iyyun su suka rasa rumfunan su.

1. Atiku Abubakar:

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya rasa rumfar sa a garin Jada, jihar Adamawa inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashe zaben.

2. Yemi Osinbajo:

Wani sakamakon zaben da ya baiwa al'umma da dama mamaki haka zalika shine na faduwa rumfar da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yayi a rumfar sa can jihar Legas a zaben na ranar Asabar.

3. Cif Olusegun Obasanjo:

Shi ma dai tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Obasanjo ance jam'iyyar da yake goyon baya ta PDP a zaben shugaban kasa ta fadi a rumfar sa a can garin Ota na jihar Ogun.

4. Ibrahim Dankwambo:

Duk dai dai ance shi yaci zaben sa na takarar kujerar Sanata da yake yi, amma jam'iyyar APC ce akace ta lashe zaben shugaban kasa a rumfar gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo.

5. Sanata Shehu Sani:

Sanata Shehu Sani wanda yayi kaurin suna sosai a majalisar dattawa da kuma yasha rikici da gwamnan jihar Kaduna har ya fice daga jam'iyyar APC zuwa PRP shima ance ya sha kaye a rumfar da ya kada kuri'ar sa a garin Kaduna.

6. Injiniya Buba Galadima

7. Barista Ibrahim Shehu Shema

8. Sanata Godswill Akpabio

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel