KAI TSAYE: Sakamakon zabe daga jihohin Bauchi, Gombe da Filato

KAI TSAYE: Sakamakon zabe daga jihohin Bauchi, Gombe da Filato

SHIMFIDA: A yayin da aka kammala kad'a kuri'u a wasu sassa na jihohi 36 na kasar Nigeria, ciki kuwa har da jihohin Bauchi, Gombe da Filato, tuni aka fara tattara kuri'u tare da kidaya su a wasu rumfunan zabe na jihohin.

Legit.ng Hausa ta shirya kawo maka labarai kai tsaye, dangane da tattara kuri'u da kuma kidayarsu a jihohin Bauchi, Gombe da Filato, domin baka damar sanin halin da zaben jihohin ya ke ciki. Sannan zamu kawo maku cikakken sakamakon zaben jihohin daga bakin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC.

HATTARA: Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ce kadai ke da ikon tattara kuri'u da fadin sakamakon zabe. Bayanai kan sakamakon kuri'un da aka kad'a a mazabun da zaka karanta a wannan shafin ba daga hukumar INEC ya ke ba. Legit.ng Hausa ba za ta iya tantance gaskiyar sakamakon ba.

KARANTA WANNAN: KAI TSAYE: APC ta sha kasa a kujerar Sanatan Katsina ta Arewa, rumfar zaben Buhari

Duba yadda ake ci gaba da tattara sakamakon zabe da kidaya a wasu sassa na kasar...

LAHADI 24/2/2019

4:00pm-6:00pm

Jam'iyyar PDP ta lallasa APC da tazarar kuri'u 20670, a mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa, mazabar da kakakin majalisar wakilan tarayya Yakubu Dogara ke wakilta.

PDP 72,334

APC 51,664

11:00am-1:00pm

 • Sakamakon zaben akwatin cikin fadar sarkin Bauchi.

President

APC= 988

PDP= 113

Senate.

APC= 112

PDP= 86

House of Representatives

APC= 108

PRP= 824

PDP= 166.

 • Isawa Azare: Zabi Ward, Giade LGA, Bauchi State

Presidential

APC = 1,663

PDP = 426

 • Jekadafari Ward, Gombe State, Collation Centre:

Presidential

APC = 12,754

PDP = 1,135

Sanetor

APC = 10,566

PDP = 3,923

House of Representatives

APC = 9,777

PDP = 2,446

 • Pantami Ward in Gombe State

Presidential Election

APC 11, 429

PDP 674

Senate

APC 8763

PDP 3394

House of Representatives

APC 8989

PDP 2313

 • BAUCHI: Dass Local Government. PU 003, Tsafi, Durr Ward

PRESIDENT

APC = 275.

PDP = 43

9:00am-10am:

 • Plateau South Senatorial District :Lagan polling Unit (Waroh Ward ,Langtang North LGA)

President

APC 281

PDP 257

Senate

APC 281

PDP 281

House of Representatives

APC 261

PDP 281

 • Sakamakon zaben Jekadafari Ward, Gombe State, Collation Centre:

Presidential

APC = 12,754

PDP = 1,135

Sanetor

APC = 10,566

PDP = 3,923

House of Representatives

APC = 9,777

PDP = 2,446

8:00am-9:00am:

 • Sakamakon zaben rumfar zaben Yakubu Dogara, kakakin majalisar wakilan tarayya

(Gwarangah Unit, Bogoro C Ward, karamar hukumar Bogoro, jihar Bauchi.

Presidential - PDP 1080, APC 47

Senate PDP - 1105, APC 39

House of Reps - PDP 1159, APC 8

-----------------------------------------------------------------------------------------------------------------------

5:00pm-7:00pm:

Rahotannin da muke samu na daga jihar Bauchi, na nuni da cewa akwai wasu rumfunan zabe da ba a gudanar da zabe ba a karamar hukumar Katagum jihar Bauchi saboda rashin kayan zabe. Sai dai har yanzu ba a san hakikanin adadin rumfunan zaben da lamarin ya shafa ba.

 • PU 061, Makama Sarkin Baka, Bauchi LGA, Bauchi South

Presidential election results

APC: 218

PDP: 26

Senatorial election results

APC: 91

PDP:95

PRP: 51

NNPP: 8

Bauchi Federal Constituency election results

PRP:

APC: 50

PDP: 23

SDP: 165*

 • JAURO ABARE II: Gov Dankwambo's Senatorial Constituency! Jihar Gombe

Presidential

APC 200, PDP 13

Senate: APC 158, PDP 57

 • Hill Station Junction, PU 023, Janta Adamu Ward, Jos North LGA, Plateau State

Zaben shugaban kasa:

APC- 7; PDP- 34 votes.

Senate

APC - 6, PDP - 34; PRP - 1

House of Representatives

APC -7, PDP - 32, SDP 1, NPN - 1, ADP -1.

Daga cikin mutane 138 da suka yi rejista, 42 ne kadai suka yi zabe

 • Bauchi: PU 061, Makama Sarkin Baka, Bauchi ta Kudu

Zaben shugaban kasa:

APC: 218

PDP: 26

 • Karamar hukumar Ningi, jihar Bauchi; Kofar Alhaji Abdu Yaro..004

APC=338, PDP=112

Lalatattu: 36

 • Karamar hukumar Ningi, jihar Bauchi; Kofar Gwarami......003

APC=369, PDP=70.

Lalatattu: 02

 • Mazabar Gwamnan jihar Gombe; Jauro Abare II

Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 200, inda ta lallasa jam'iyyar PDP, wacce ta samu kuri'u 13 a matakin kujerar shugaban kasa. A matakin kujerar Sanata kuwa, APC ta samu kuri'u 158 yayin da PDP ta samu 57. A kujerar majalisar wakilan tarayya, APC ta samu kuri'u 152 yayin da PDP ta samu kuri'u 52.

2:00pm-3:00pm:

HOTUNA: Gwamnan jihar Filato, Solomon Lalong tare da uwar gidansa, sun kad'a kuri'arsu a rumfar zabensa da ke garin Jos.

KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato

KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato
Source: Twitter

KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato

KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato
Source: Twitter

HOTUNA: Gwamna M.A Na Jihar Bauchi Tare Da Matansa Hajiya Hadiza Abubakar Da Barista Aisha Abubakar Yayin Da Suke Jefa Kuri'arsu A Mazabarsa Dake Jahun Garun Galadima

Bayan haka Gwamnan ya yaba da yadda zaben ke gudana, sannan ya kuma yi kira ga al'ummar da su kasance masu bin doka da oda don ganin an kammala zaben cikin lumana.

KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato

KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato
Source: Twitter

KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato

KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato
Source: Twitter

KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato

KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato
Source: Twitter

1:00pm-2:00pm:

Shugaban kungiyar Izala reshen jihar Jos, Sheik Sani Yahya Jingir, ya bi sahun dandanzon al'ummar da ke a rumfar zabensa, inda aka tantance shi kana ya kad'a kuri'arsa a karamar hukumar Kanam, jihar Filato.

Al'ummar mazabar Fuloti dake cikin garin Jingir dake karamar hukumar Bassa ta Jihar Filato, suna cigaba da kada kuri'ar su amma zaben yana tafiyar hawainiya.

A jihar Bauchi, har zuwa karfe 11:22 na safiya, ba a soma tantance masu kad'a kuri'a a rumfar zabe ta Sakwa da ke karamar hukumar Zaki ba. Sai dai an alakanta hakan da lalacewar na'urar tantance masu zabe, sanadin da ya jawo jama'a na barin rumfar zaben.

Har zuwa karfe 11:00 na safe, rufar LG VET da ke jihar Bauchi, ba'a kawo kayan zabe ba ballan tana afara kada kuri'a.

Rahotanni sun bayyana cewa rumfar zabe ta Malam Bashar mai Tafsir da ke karamar hukumar Katagum (Azare) a jihar Babu, har zuwa karfe kusan 10-11 na safiya, jami'an zabe ba su isa wajen ba, duk da cewa akwai masu kad'a kuri'a da ke zaman jira.

Mazabar masakar makafi dake kan titin Gombe, jihar Bauchi kenan, inda sai da bayan karfe 8 na safiya ma'aikatan zabe suka isa rumfar zaben.

11:00am-12:00pm:

HOTUNA: Kakakin majalisar wakilan tarayya, Hon. Yakubu Dogara ya kad'a kuri'arsa a rumfar zabensa ta Gwaranga mai lamba 007, karamar hukumar Bogoro, jihar Bauchi.

KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato

KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato
Source: Twitter

KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato

KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato
Source: Twitter

KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato

KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato
Source: Twitter

10:00am-11:00am:

Labarin da muke samu, daga jihar Bauchi, na nuni da cewa har yanzu ba a fara tantance masu kad'a kuri'a a rumfar zabe da ke cikin sansanin sojoji na Shadawanka da ke cikin kwaryar Bauchi ba. Haka zalika, akwai rumfunan zabe da har yanzu ba a rarraba masu kayayyakin zaben ba.

Rahotannin da muke samu daga gundumar Hassan Manzo, Yerwa Gana, karamar hukumar Gombe da ke cikin jihar Gombe, na nuni da cewa masu kad'a kuri'a na ci gaba da duba sunayensu tare da hawa layi a rumfar zabe mai lamba 005, inda ake sa ran fara tantancewa tare da kad'a kuri'a. Zaben na gudana lafiya a jihar Gombe.

9:00am-10:00am:

HOTO: Masu kad'a kuri'a a wata mazaba a jihar Bauchi suna amfani da duwatsu domin kama layi, yayin da su ke shiga inuwa domin samun mafaka daga yanayin hazo da garin ya ke ciki.

KAI TSAYE: Yadda masu kad'a kuri'a ke amfani da duwatsu domin kama layi a Bauchi

KAI TSAYE: Yadda masu kad'a kuri'a ke amfani da duwatsu domin kama layi a Bauchi
Source: Twitter

Rahotannin da muke samu daga karamar hukumar Gamawa, jihar Bauchi, na nuni da cewa har yanzu jami'an hukumar zabe ta kasa INEC, ba su kai ga isa wasu rumfunan zabe ba, duk da cewa akwai masu kad'a kuri'a da suke kan jiran fara zaben.

An fara kad'a kuri'a a rumfar zabe mai lamba 009 da ke cikin makarantar firamare ta Manu, karamar hukumar Ningi, jihar Bauchi. Sai dai rahotanni sun bayyana cewa har yanzu babu wani jami'in tsaro a akwatunan zabe hudu da ke yankin.

8:00am-9:00am:

Bisa rahotannin da muke samu, tuni masu kad'a kuri'a a jihohin Bauchi, Gombe da Filato suka kasance a akwatunan mazabarsu, yayin da hukumar INEC ta isa mafi akasarin akwatunan zaben domin fara tantance masu kad'a kuri'ar.

Sai dai akwai garuruwa da dama a cikin jihohin ukku, da har yanzu hukumar INEC ba ta kai ga isa rumfunan zaben ba, ana sa ran isowar jami'an hukumar wadannan rumfunan zabe a kowanne lokaci.

Jami'an tsaro na ci gaba da sintiri a lungu da sako na jihohin, domin tabbatar da tsaro da kuma ganin cewa zaben ya gudana ba tare da wani tashin hankali ko fuskantar matsalar tsaro ba.

Sai dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta bayyana cewa ba zata iya buga wasu sabbin katunan zabe na din-din-din ga masu kad'a zaben da suka rasa katin zabensu a gobarar da ta barke a hukumar zaben a kwanakin baya a jihar Filato.

HOTO 1: Masu kad'a kuri'a na ci gaba da zaman jiran fara tantancewa da kad'a kuri'arsu a Billiri, mazabar Gombe ta Kudu.

KAI TSAYE: Billiri, mazabar Gombe ta Kudu

KAI TSAYE: Billiri, mazabar Gombe ta Kudu
Source: Twitter

HOTO 2 - 4: Yadda zabe ke gudana kai tsaye a akwatin fadar jihar Bauchi. Cikin makarantar firamare ta Shekal.

Jihar Bauchi: Masu bautar kasa (NYSC) na shirya kayan zabe a fadar Bauchi

Jihar Bauchi: Masu bautar kasa (NYSC) na shirya kayan zabe a fadar Bauchi
Source: Facebook

KAI TSAYE: Ana ci gaba da tantance masu kad'a kuri'a a fadar Bauchi

KAI TSAYE: Ana ci gaba da tantance masu kad'a kuri'a a fadar Bauchi
Source: Facebook

KAI TSAYE: Masu kad'a kuri'a na ci gaba da zaman jiran tantancewa da kad'a kuri'a a Bauchi

KAI TSAYE: Masu kad'a kuri'a na ci gaba da zaman jiran tantancewa da kad'a kuri'a a Bauchi
Source: Facebook

KU LURA: Ci gaba da kasancewa tare da wannan shafin, zamu kasance masu kawo maka karin bayani akai-akai, bukatarmu shine ka yi 'refreshing' shafin lokaci-zuwa-lokaci, domin ci gaba da samun bayanai na gaskiya kan yadda zabukan ke gudana a wadannan jihohin guda ukku.

KA SANI: Idan kana da wani rahoto da kake son aikowa kai tsaye, da ya shafi jihohin Bauchi, Gombe da Filato, kana da damar yin hakan, amma sai idan kana da hujjoji na rahotonka, walau bidiyo ko hotuna. Idan ka cika wad'an nan ka'idojin, aika labarinka ta WhatsApp, zuwa ga lambar waya: 08026364102.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel