Allura-cikin-ruwa: Jerin jahohi 14 da za su zama tamkar filin daga ga Atiku da Buhari

Allura-cikin-ruwa: Jerin jahohi 14 da za su zama tamkar filin daga ga Atiku da Buhari

Yayin da ya rage saura 'yan awanni 'yan Najeriya su fita domin su kada kuri'ar su da zata basu damar zabar wanda zai jagoranci kasar har shekaru hudu masu zuwa, harkokin siyasa na cigaba da yin zafi a jahohi da dama kamar dai yadda muka samu daga majiyoyin mu.

Kamar yadda muka samu dai, manyan 'yan takarkarin shugabancin kasar kuma daga manyan jam'iyyun ne dai na PDP watau Atiku Abubakar da kuma APC watau Muhammadu Buhari ne ke kan gaba a dukkan alamu.

Allura-cikin-ruwa: Jerin jahohi 14 da za su zama tamkar filin daga ga Atiku da Buhari
Allura-cikin-ruwa: Jerin jahohi 14 da za su zama tamkar filin daga ga Atiku da Buhari
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: An ga wasu sojoji suna yiwa Buhari kamfe

Sai dai Legit.ng Hausa ta tattaro mana wasu jahohin da ake sa ran zaben a tsakanin manyan jam'iyyun zai yi zafi sosai watakila ma ya bayar da mamaki idan an kammala saboda wasu dalilai.

Jahohin dai da za su dauki hankali sun hada da: Adamawa, Rivers, Katsina, Benue, Borno, Kano, Kwara, Imo, Lagos, Akwa Ibom, Ondo, Oyo, Jigawa da kuma Kaduna.

A wasu jahohin kamar Adamawa da Katsina dake zaman jahohin da 'yan takarar suka fito, ana sa ran zaben su ya bayar da mamaki musamman ma ganin yadda su kan su 'yan takarar suka mayar da hankalin su sosai a kan su.

Jahohi kuma kamar Benue da Kaduna, ana tunanin baya ga kabilanci da addinanci da zai iya yin tasiri a zaben, akwai matsalar tabarbarewar tsaro da ake tunanin zai sa zaben yayi zafi.

Su kuwa a bangaren jahohin Kwara, Kano da Akwa Ibom, ana ganin cewa sauyin shekar wasu jiga-jigan siyasa a jahohin zai yi matukar tasiri akan masu zabe da kuma wanda za su zaba.

A dayan bangaren kuma rikicin jam'iyyun dake a jahohin Imo, Legas, Ondo da Oyo shima zai yi matukar tasiri a zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel