Ta faru ta kare: Kungiyoyin Yarabawa 25 sun yanke hukunci, sun goyi bayan Buhari/Osinbajo

Ta faru ta kare: Kungiyoyin Yarabawa 25 sun yanke hukunci, sun goyi bayan Buhari/Osinbajo

Akalla kungiyoyin ci gaban al'ummar Yaraba guda 25 ne suka yi kira ga daukacin mambobinsu da suka kai miliyan 20, da ke a fadin shiyyar Kudu maso Yamma, da suka hada da jihohin Kogi, Kwara da Delta, da su fito kwansu da kwarkwatarsu a ranar Asabar mai zuwa domin kad'a kuri'arsu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo.

Kungiyoyin a cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Alhamis, sun umurci jihohi Yaraba da su fito "kwansu da kwarkwatarsu domin zabar shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, wanda shi daya daga cikinmu ne a ranar 23 ga watan Fabreru."

A cikin sanarwar mai taken 'Ku tashi tsaye', kungiyoyin sun ce sun dauki wannan matakin na goyon bayan Buhari biyo bayan jin ra'ayoyin Yarabawa manoma, masu kirkira da fasaha, ma'aikata da ma sauran gama gari da ke birni da kauyuka, da suka hada da mata da maza da ma kananan yara kan wanda za su zaba a zaben mai zuwa.

KARANTA WANNAN: Akwai makarkashiya: Cafke sanata Rafiu Ibrahim ana gobe zabe - Hadimin Saraki

Ta faru ta kare: Kungiyoyin Yarabawa 25 sun yanke hukunci, sun goyi bayan Buhari/Osinbajo

Ta faru ta kare: Kungiyoyin Yarabawa 25 sun yanke hukunci, sun goyi bayan Buhari/Osinbajo
Source: Facebook

"Muna goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo, wanda farfesa ne a fannin shari'a, ko a cikin kusan shekaru hudu ya tabbatar da sanin makamar aikinsa, tare da gudanar da rayuwarsa bisa tsari na gaskiya da amana, hakika saboda shi muka yanke wannan shawarar domin ci gaban kasar Yarabawa da al'ummarta."

Kungiyoyin ta kuma ce sun gamsu da takarar Buhari/Osinbajo duba da irin kyakkyawan kudurin da suke da shi akan kasar da kuma yin Allah wadai da 'yan siyasar da ke kokarin ganin cewa sun tarwatsa rayuwar Yarabawa a kasar.

Kungiyoyin sun kuma yi martani ga jam'iyyar adawa na cewar za ta sake fasalin kasar, wanda a cewarsu hakan zai kawo tasgaro babba ga ci gaban al'ummar Yarabawa. Sun kuma ce tsarin APC shi ne kadai canjin da zai haifar da d'a mai ido a kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel