Dahiru Bauchi ya yi tir da Musulmai masu zagin Musulmai a kan siyasa

Dahiru Bauchi ya yi tir da Musulmai masu zagin Musulmai a kan siyasa

Daya daga cikin fitattun malaman addinin musulunci a Najeriya kuma jagoran mabiya Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Bauchi, ya yi tir da babi’un wasu malaman addini da ke tsine wa musulmai a kan bambancin siyasa kawai.

Sheikh Dahiru Bauchin ne ya kuma nuna rashin jin dadin sa a lokacin da Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara ya kai masa ziyara a gidan sa.

Malamin ya shaida wa mabiyan sa zaman lafiya da sauran al’umma da ake zaune tare, musamman wadanda ba addinin su daya ba. Ya kuma yi kira da a kara yin nesa da ra’ayin rikau da kullatar juna.

A cewar sa, da ya zabi dan Izala wanda bai ganin girman dan Tijjaniya kuma bai yarda da cewa dan Tijjaniya musulmi ba ne, to har gara ya zabi Kirista.

Yayin da ya yi kira ga al’ummar Bauchi su guji siyasar raba kan mabiya addinai, jagoran na Tijjaniya ya kuma yi kira ga al’ummar mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa su sake zaben Dogara, saboda gagarimin ciyar da mazabar sa da ya yi.

Dahiru yace kowa ya shaida yadda Dogara ke siyasar ciyar da jama’a da kuma mazabar sa tare da rashin cusa addinanci a zukatan siyasar jama’a.

Da ya ke jawabin godiya, Dogara ya gode da irin addu’ar da Sheikh Dahiru Bauchi ya yi masa.

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel