Magada-Annabawa: Sheikh Sani Rijiyar Lemo yace bai kamata malamai su shiga siyasa ba

Magada-Annabawa: Sheikh Sani Rijiyar Lemo yace bai kamata malamai su shiga siyasa ba

Daya daga cikin malaman Ahalussuna a Najeriya Sheikh Sani Rijiyar Lemo ya yi tsokaci game da shigar malaman addini cikin siyasa tsundum inda yace sam hakan bai dace ba a nashi ra'ayin da kuma fahimtar sa a addinance.

Shehin malamin ya bayar da wannan fatawar a lokacin da yake gudanar da karatu ga dumbin mabiyan sa a masallacin sa dake jihar Kano.

Magada-Annabawa: Sheikh Sani Rijiyar Lemo yace bai kamata malamai su shiga siyasa ba

Magada-Annabawa: Sheikh Sani Rijiyar Lemo yace bai kamata malamai su shiga siyasa ba
Source: Facebook

KU KARANTA: Na yi nadamar tsinewa makiyan Buhari - Sheikh Giro

Legit.ng Hausa ta samu cewa malamin yace bai kamata ace malamai sun shiga harkokin siyasa ba har ta kai ga suna kama suna wajen fadawa mabiyan su wanda ya kamata su zaba a ranar zabe.

Sheikh Rijiyar Lemo ya kara da cewa siyasar nan duka domin neman duniya ake yin ta domin kuwa babu wanda zaka zaba don ya jagorance ka a addinance sai don samun maslahar harkokin duniya kamar tsaro, abinci da kuma ingantattar rayuwa.

Ya cigaba da cewa shi malamin addini kamata yayi kawai ya fadakar da mutane akan siffofin wanda ya kamata su zaba sai ya kyale su suje su zabi wanda ya kwanta masu a rai.

Wannan fatawar dai ta malam Rijiyar lemo ta zo ne dai dai lokacin da kawunan malaman Izala da ma mabiyan su suka rarrabu akan siyasar zabe mai zuwa inda wasun su suka ce Shugaba Buhari za su zaba wasu kuma suka ce Atiku za su zaba.

Ga dai bidiyon fatawar nan tashi:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel