Kiwon lafiya: Kwararriyar likita ta gargadi yan siyasa kan samun tabin kwakwalwa

Kiwon lafiya: Kwararriyar likita ta gargadi yan siyasa kan samun tabin kwakwalwa

Wata kwarrariyar likitan kwakwalwa, Dakta Tomi Imarah, ya gargadi al'umma da su karbi sakamakon zabe yadda ya zo musu don kaucewa samun matsalar kwakwalwa.

Likita Imarah, mammalakiyar shafin yanar gizo da ke bada shawarwari kan yadda al'umma za ta kula da kwakwalwa mai suna "Dr. Tomi Haven", ya bayyana hakan ne a wata hira da ya gabatar da kamfanin dillancin labarai, NAN a ranar Lahadin da ta gabata

A cewar ta, 'yan siyasan da suka fadi zabe na da barazanar kamuwa da matsalar kwakwalwa sakamakon zafin karbar sakon faduwar da zai zo musu.

Haka suma wadanda suka yi nasara na da barazanar kamuwa da irin wannnan matsalar kwakwalwa sakamakon murna da zai buge su na lokaci guda sakamakon nasarar

"A lokuta da dama muna dauka cewa 'yan siyasa sun karbi rashin nasara a yayin da ta zo, kuma su ci gaba da rayuwarsu kamar dai babu wani abu da ya faru.

"Ko shakka babu, rashin nasarar nasu na nuna cewa sun samu rashin karbuwa ne a wajen al'ummarsu, kuma hakan dole zai yi tasiri a cikin ransu a duk lokacin da abin ya dawo musu.

"Kamar dai kowa, 'yan siyasa basu da wata kariya daga shiga damuwa.

"Wannan kuwa ya hada da shiga wani irin yanayi, rashin kuzari, rashin gamsuwa, bacin rai da rashin karsashi  da dai sauransu,|" a cewar Likita Imarah.

Ta cigaba da cewa, wannan ko shakka babu zai shafi kudire-kudire da manufofin da za su gabatar a ofishinsu akalla na shekarar farko.

"Dakta Ashley Weinberg na sashen ilimin halayar dan adam na jami'ar Salford a Burtaniya ta ya gabatar da wani bincike na shekaru 15 akan wadanda ke neman zaman 'yan takarar majalisar kasar ta Burtaniya.

"Binciken nasa ya bayyana cewa da dama daga cikin 'yan majalisar na samun matsaloli da ke da alaka da kwakwalwa da suka hada da sauyawar halayya, rashin samun barci, gajiya da kasala ta dindindin na akalla shekara guda bayan sun yi nasarar shiga ofis kafin daga baya su mike su cigaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

'"Yan siyasar Nijeriya ma nasu da wata kariya da za ta hana su fada wa irin wannan yanayin sakamakon sauyin rayuwa da suke samun kansu a ciki.

"Amma kuma, illar rashin nasara ya fi tsanani sama da na wadanda suka samu nasara.

"Sai dai kuma babu wani tsari da a ke yi na samar da wani yanayi da zai zama riga kafi ga 'yan siyasa kafin da ma bayan zabe don kulawa da yanayinsu kan yadda za su shiga ofis bayan sun yi nasara, da kuma yadda za su tunkari rayuwa in sun yi rashin nasara," inji Imarah.

Wannan rubutu na likitar kwakwalwa nada muhimmanci matuka musamman yanzu da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa, yan majalisan dattawa, yan majalisar wakilan tarayya a ranar 23 ga watan Febrairu, 2019 a Najeriya.

Daga bisani a gudanar da zaben gwamnonin jihohi 29 a fadin tarayya da kuma yan majalisun dokokin jihohi 36 a ranar 9 ga watan Maris, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel