Sheikh Daurawa ya jagoranci malamai sama da 100 zuwa yiwa Kwankwaso mubayi'a a Kano

Sheikh Daurawa ya jagoranci malamai sama da 100 zuwa yiwa Kwankwaso mubayi'a a Kano

Sheikh Aminu Daurawa ya jagoranci sama da malamai 100 suka je gidan Rabiu Musa Kwankwaso don nuna goyan bayansu gareshi tare da nesanta kansu ga abubuwan da wasu malamai suke fada a kansa.

Sanata Kwankwaso dai dake zaman jagoran darikar siyasa ta Kwankwasiyya a jihar ta Kano da sauran sassan kasar nan ya sha caccaka daga sassan kasar nan da dama biyo bayan fitar faifan saudi dauke da muryar sa yana sukar malaman addini da ke shiga tsundum a cikin siyasa.

Sheikh Daurawa ya jagoranci malamai sama da 100 zuwa yiwa Kwankwaso mubayi'a a Kano

Sheikh Daurawa ya jagoranci malamai sama da 100 zuwa yiwa Kwankwaso mubayi'a a Kano
Source: UGC

KU KARANTA: Buhari zai iya faduwa zaben gobe - Jigon APC

Wannan batu nasa bai yi wa Malaman Izala dadi ba cikinsu kuwa har da Sheikh Abdullahi Pakistan da Sheikh Giro Argungun da ma wasu da dama, inda suka zargi Kwankwaso da aibata sunar Annabi SAW.

Sai dai kuma a wani abu da ya yi kama da gaskata maganar Kwankwaso, Sheikh Daurawa ya jagoranci limamai sama da dari zuwa gidan Kwankwaso don su jaddada goyon bayansu ga shi Kwankwason.

Daurawa ya bayyana cewa da gangan Malaman Izala suka juya kalaman Kwankwaso don su harzuka magoyaba bayansu su tsani Kwankwaso.

Wasu manyan malamai daga cikin wadanda suka yi wa Daurawa rakiya sun hada da: Sheikh Sani Ashir, Sheikh Malam Nazifi, Sheikh Abubakar Kandahar da Sheikh Gwani Sanusi.

Sauran sun hada da: Sheikh Alkali Mustapha, Sheikh Bazallah Kabara, Sheikh Buba Jada, Sheikh Isma’ila Mangu, Shiekh Malam Kabiru da dai sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel