Yariman Saudiyya mai jiran gado ya hau saman rufin dakin Ka'aba

Yariman Saudiyya mai jiran gado ya hau saman rufin dakin Ka'aba

Yariman kasar Saudiyya mai jiran gado Muhammad bin Salman ya hau saman rufin dakin Ka'aba a lokacin da ya kai ziyara garin Makkah mai tsarki.

An tattaro cewa, Yariman ya ziyarci garin Makkah ne saboda ya duba sabbin ayyukan da ake gudanarwa a Dakin Ka’aba.

Bin Salman da ya halarci wanke Dakin Ka'aba da aka saba yi tare da jami'an tsaro 600 dake kare shi ya fara sumbatar Hajarul Aswad inda daga nan kuma ya hau matattakalar tare da shiga cikin dakin Ka'aba.

Yariman Saudiyya mai jiran gado ya hau saman rufin dakin Ka'aba
Yariman Saudiyya mai jiran gado ya hau saman rufin dakin Ka'aba
Asali: Depositphotos

Yarima bin Salman ya yi Sallah a cikin Ka'aba inda ya dauki wani tsumma tare da yin goge-goge, sannan kuma sai ya hau saman rufin Dakin Mai Tsarki wanda abu ne da ba a saba gani ba.

KU KARANTA KUMA: Nasara ko fadu wa: Buhari ya roki Atiku ya karbi sakamakon zabe

Hawan Yariman saman Dakin Ka'aba ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta na yanar gizo.

An samu tarihin cewar daga cikin Halifofin Daular Abbasiyya Abu Ja'afar Al-Mansur ya taba hawa rufin Dakin.

A yanzu dai ma'aikata na hawa saman Dakin don tsaftace shi a lokacin da aka yi ruwan sama ko kuma za a sauya rigarsa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel