Da duminsa: An nemi Oshiomhole da Tinubu an rasa a filin gangamin APC na Abuja

Da duminsa: An nemi Oshiomhole da Tinubu an rasa a filin gangamin APC na Abuja

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu yanzu na nuni da cewa jam'iyyar APC ta kaddamar da yakin zabenta a babban birnin tarayya Abuja. Gangamin yakin zaben wanda ke kan gudana a filin wasanni na 'Eagles Square', ya samu halartar minsitan FCT, Mohammed Bello da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Sauran wadanda suka halarci gangamin sun hada da shugabar mata ta jam'iyyar APC ta kasa, (Hajiya) Salamatu Umar-Eluma da kuma gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, da dai sauransu.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: PDP ta maka INEC kotu kan dagewa akan lallai sai ta yi amfani da 'Card Reader'

Da duminsa: An nemi Oshiomhole da Tinubu an rasa a filin gangamin APC na Abuja

Da duminsa: An nemi Oshiomhole da Tinubu an rasa a filin gangamin APC na Abuja
Source: Facebook

Sai dai har zuwa yanzu, an nemi jagoran jam'iyyar na kasa Bola Ahmed Tinubu da shugaban jam'iyyar na kasa Adams Oshiomhole an rasa.

A yayin da ya rage saura kwanaki ukku babban zabe na kasar, jam'iyyun siyasa na ci gaba da karkare rangadin yakin zabensu zuwa awanni 24 na ranar keke-da-keke.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel