Wamakko na shirin karban kwamishinonin PDP 4 zuwa APC a Sokoto

Wamakko na shirin karban kwamishinonin PDP 4 zuwa APC a Sokoto

Jam’iyyar All Progressive Congress (APC) gab da sake yin babban kamu inda kwamishinoni masu ci a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ke shirin komawa jam’iyyar, a cewar shugaban sanatocin Arewa, Sanata Aliyu Magatakarda.

Hakan na kunshe a cikin wani jawabi daga mataimakinsa na musamman kan kafofin labarai, Bashir Rabe Mani wanda ya gabatarwa yan jarida a Sokoto.

Jawabin ya bayyana cewa, Sanata Wamako wanda ke wakiltan yankin arewacin Sokoto yayi agana ne yayinda yake kaddamar da ofishin yakin neman zaben jam’iyyan a unguwan Filin ‘Yan Shanu, yankin Adar, a karamar hukumar Sokoto North da ke jihar.

A cewar Sanata Wamakko, nan ba da dadewa ba za a bayyana sunayen sabbin mambobin APC din ga mutanen jihar.

Wamakko na shirin karban kwamishinonin PDP 4 zuwa APC a Sokoto

Wamakko na shirin karban kwamishinonin PDP 4 zuwa APC a Sokoto
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewa, wannan abun cigaban ya daukaka kauna, da girmamawa da kuma rayar da mutanen jihar tare da daukaka da suka nunawa jam’iyyar APC da yan takaranta a dukkan matakai.

Sanata Wamakko ya cigaba da bayyana cewa kwanakin nan mutanen jihar da dama sun sauya sheka zuwa jam’iyyar, musamman daga PDP.

KU KARANTA KUMA: Kada ku sa mu cikin masu goyon bayan Buari – Kungiyar Musulunci

Yayinda yake bayyana ra’ayinsa, akan muhawarar masu takaran gwamna wanda BBC sashin Hausa ta shirya yace, “wannan ya nuna cewa dan takaranmu, Alhaji Ahmed Aliyu Sokoto baya da rashin kwarewa a fagen siyasa kamar yanda wasu suke tunani.”

Haka zalika, Sanata Wamakko ya bukaci mutanen jihar dasu zabi yan takaran jam’iyyar APC a dukkan matakai na zaben kasa da za a gudanar kwanan nan.

Alhaji Ahmed Aliyu Sokoto ya sha alwashin karfafa cigaba da Sanata Wamakko ya kawo a lokacin da ya rike mukamin gwamna a jihan tsakanin 2007 da 2015.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel