NBA ta yi Allah wadai da cin mutuncin Qur’ani a Zamfara, tace ya zama dole a hukunta wadanda suka aikata laifin

NBA ta yi Allah wadai da cin mutuncin Qur’ani a Zamfara, tace ya zama dole a hukunta wadanda suka aikata laifin

Kungiyar lauyoyin Najeriya reshen jihar Zamfara ta yi Allah wadai da rahoton cin mutuncin littafi mai tsarki wato Qur’ani a Gusau, sannan tayi kira ga bincike domin gano wadanda suka aikata laifin.

Kungiyar ta NBA a wani taron manema labarai a Gusau a ranar Litinin, 11 ga watan Fabrairu tace lamarin abun bakin ciki ne da damuwa.

Bello Galadi, Shugaban kungiyar, yace mambobin kungiyar sun sake duba lamarin a wani taro a ranar Asabar, 9 ga watan Fabrairu.

NBA ta yi Allah wadai da cin mutuncin Qur’ani a Zamfara, tace ya zama dole a hukunta wadanda suka aikata laifin
NBA ta yi Allah wadai da cin mutuncin Qur’ani a Zamfara, tace ya zama dole a hukunta wadanda suka aikata laifin
Asali: UGC

Shugaban kungiyar yace: “Mun yi Allah wadai da wannan lamari sosai. Wannan abu ya fara wuce gonad a iri, kamar yadda ya sa faruwa a lokutan baya, inda aka gano shafukan Al-Qur’ani a bayin wata makarantar gwamnati da ke Sabon gari, Gusau.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019 zai zamo zabena na 5 kuma na karshe, ba zan wofantar da kundin tsarin mulki ba - Buhari

“Abun bakin ciki ne ganin cewa yan kwanaki da suka gabata an sake ganin littafin mai tsarki a wani bayin wani asibiti da ke Gusau.”

Galadi ya bayyana cewa akwai bukatan a kara karfin bincike a kasar sannan cewa ayi gaggawan tsaurara mataka tsaro a jihar domin kamo wadanda suka aikata hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel