Allah-ya-isa: Shugaba Buhari ya kai karar barayin 'yan PDP wajen Allah

Allah-ya-isa: Shugaba Buhari ya kai karar barayin 'yan PDP wajen Allah

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ce Allah ne kadai zai iya yiwa barayin 'yan jam'iyyar adawa ta Peoplees Democratic Party (PDP) da suka tafka sata ta tashin hankali lokacin da suke kan madafun iko hisabi.

Shugaban kasar dai yayi wannan kalaman ne lokacin da yake labartawa wasu mambobin kunyoyin dake goyon bayan tazarcen sa irin cikin halin takaicin da ya tsinci kasar a shekarar 2015 bayan lashe zaben sa.

Allah-ya-isa: Shugaba Buhari ya kai karar barayin 'yan PDP wajen Allah
Allah-ya-isa: Shugaba Buhari ya kai karar barayin 'yan PDP wajen Allah
Asali: Twitter

KU KARANTA: Matasa sun lalata allunan kamfe din APC a Borno

Legit.ng Hausa ta tsinkayi cewa shugaban kasar wanda ya rika magana cikin takaici ya bayyana cewa jam'iyyar ta adawa ta Peoplees Democratic Party (PDP) ba karamar ta'asa ta tafka ba a tsawon shekaru 16 da ta yi tana mulkar Najeriya.

Ya kara cewa duk da yake idan aka kiyasta, jam'iyyar ta rika sayar da gangar danyen mai akan farashin $100 ne a lokacin mulkin ta, jam'iyyar bata tsinanawa kasa komai ba tsawon lokacin sai ma dai satar da suka yi ta yi ba kama hannun yaro.

Daga karshe sai shugaban kasar yace shi ba abun da zai ce da 'yan PDP din sai Allah ya isa domin shine kadai zai iya sakawa 'yan Najeriya cutar su da jam'iyyar ta Peoplees Democratic Party (PDP) tayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel