Ba wasa: Igbo, Hausa, Fulani sun sha alwashin tunbuke Buhari ta hanyar zabar Atiku

Ba wasa: Igbo, Hausa, Fulani sun sha alwashin tunbuke Buhari ta hanyar zabar Atiku

- Bukola Saraki ya gana da Al'umar kabilu daban daban da ke zaune a jihar Kwara da suka hada da Ndigbo, Hausa, Zuru, Yoruba da na Kudu maso Kudu

- Tawagar al'ummar sun baiwa Saraki tabbacin cewa zasu fito kwansu da kwarkwatarsu domin zaben PDP a ranar 16 ga watan Fabreru da kuma ranar 2 ga watan Maris

- Saraki ya ba su tabbacin cewa zai ci gaba da fafutukar ganin walwalarsu ta bunkasa da kuma samun tagomashi a cikin iyalan gidan Saraki dama gwamnatin jihar

Al'umar kabilu daban daban da ke zaune a jihar Kwara da suka hada da Ndigbo, Hausa, Zuru, Yoruba da kuma wadanda suka fito daga Kudu maso Kudu, sun tabbatarwa shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki cewa za su bashi goyon baya tare da jam'iyyar PDP a zabe mai zuwa.

Sun tabbatarwa Saraki cewa zasu fito kwansu da kwarkwatarsu domin kad'awa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP dama sauran masu takara karkashin jam'iyyar a ranar 16 ga watan Fabreru da kuma ranar 2 ga watan Maris.

Sun bayar da wannan tabbacin ne a wani taron tattaunawa da shugaban majalisar dattijan a ofishin mazaba na ABS da ke Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

KARANTA WANNAN: Ba uwa ba riba komawarka PDP - Ganduje ya soki Kwankwaso kan fita daga APC

Ba wasa: Igbo, Hausa, Fulani sun sha alwashin tunbuke Buhari ta hanyar zabar Buhari

Ba wasa: Igbo, Hausa, Fulani sun sha alwashin tunbuke Buhari ta hanyar zabar Buhari
Source: UGC

Da ya ke jawabi a taron, shugagaban Ndigbo mazauna jihar, Sir. T.N Njoku, ya ce sun ji dadi a lokacin da Saraki ya ke gwamnan jihar da kuma kasancewarsa shugaban majalisar dattijai. "A bangaren Atiku kuwa, muna da tabbacin cewa idan muka zabe shi zai samar da ayyukan yi. Mun zabi Buhari a 2015 saboda Saraki, wannan karon za mu zabi Atiku saboda kai."

Da ya ke na shi jawabin, Sanata Saraki ya godewa wannan tawagar bisa jajurcewarsu na ci gaba da goyon bayan tsarin siyasar gidan Saraki. Haka zalika ya basu tabbacin cewa zai ci gaba da fafutukar ganin walwalarsu ta bunkasa da kuma samun tagomashi a cikin iyalan gidan Saraki dama gwamnatin jihar.

Tawagar da suka halarci taron sun je ne karkashin jagorancin Alhaji Issa AbdulRahman (Hausa, Alhaji Abiodun Jimoh (Fulani), Umar Kenna (Zuru) da kuma Chief Okugbe (Kudu maso Kudu).

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel