Boko Haram: Mazauna Madagali, Michika sun koma muhallansu bayan harin jiya

Boko Haram: Mazauna Madagali, Michika sun koma muhallansu bayan harin jiya

Mazauna karamar hukumar Madagali da Michika na jihar Adamawa sun fara komawa muhallansu bayan kimanin sa'o'i 24 da suka gudu daga gidajensu sakamakon harin Boko Haram da suka kawo yammacin Litinin.

Kwamishanan yada labarai na jihar Adamawa, Malam Ahmad Sajoh, ya bayyanawa manema labarai cewa jami'an tsaron sun dakile harin da yan ta'addan suka kawo.

Yace: "An dakile yan ta'addan a wajen tsaunin Kirchinga kusa da dajin Sambisa. Jamian tsaro sun fuskancesu kuma suka fitittikesu."

"Wannan abu ya tayar da hankalin jama'a da jita-jitan cewa sun shiga Shuwa da garin Michika, hakan yasa mutane suka gudu daga muhallansu."

"Abubuwa sun dawo dai-dai yanzu kuma mutane sun koma gidajensu."

"Zamu shiga ganawar gaggawa yanzu inda zamu samu cikakken labari kan abinda ya faru."

Ya yabawa jami'an tsaron da mazauna jihar kan jajircewa da suka nuna da yakan yan ta'addan. Yace Boko haram ba zata samu nasaran daow da hare-harensu cikin jihar ba.

KU KARANTA: Ana saura yan kwanaki zabe, kotu ta sallami dan takarar gwamnan APC

Mun kawo rahoton cewa Wasu 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram na can su na barin wuta a karamar hukumar Michika da ke jihar Adamawa.

Wata majiya ta shaida wa Legit.ng cewar mayakan kungiyar ta Boko Haram sun kai harin garin ne a daren nan.

Tsohon gwamnan jihar Legas a mukin soji, Birgediya Janar Buba Marwa, ya fito ne daga garin Michika.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel