Babbar magana: Gwamnati za ta haramta shigo da Tumatur dan kasar waje

Babbar magana: Gwamnati za ta haramta shigo da Tumatur dan kasar waje

- Ministan noma, Audu Ogbeh ya ce Gwamnatin tarayya za ta haramta shigo da tumatur dan kasar waje kafin karshen wannan shekarar

- Ogbeh ya ce haramta shigo da tumaturin zai taimaka wajen bunkasa samar da tumatur na cikin kasar da kuma amfani da shi

- Ya ce gwamnati za ta saka hannun jarin N250bn a bankin noma domin tallafawa manoma da basussuka na kayan aiki

Rahotanni sun bayyana cewa, Ministan noma, Audu Ogbeh ya ce Gwamnatin tarayya za ta haramta shigo da tumatur dan kasar waje kafin karshen wannan shekarar.

Da ya ke zantawa da manoman tumaturi na kamfanin sarrafa tumatur na Dangote da ke garin Kadawa, karamar hukumar Kura da ke jihar Kano, a ranar Litinin, Ogbeh ya ce haramta shigo da tumaturin zai taimaka wajen bunkasa samar da tumatur na cikin kasar da kuma amfani da shi.

Ya ce gwamnati za ta saka hannun jarin N250bn a bankin noma domin tallafawa manoma da basussuka na kayan aiki.

KARANTA WANNAN: Noma tushen arziki: Yadda Kano ta zama lamba daya wajen samar da tumatur

Babbar magana: Gwamnati za ta haramta shigo da Tumatur dan kasar waje

Babbar magana: Gwamnati za ta haramta shigo da Tumatur dan kasar waje
Source: Original

Emmanuel Ijewere, mataimakin kungiyar 'yan kasuwar kayan gwari ta Nigeria, ya ce jihohin shiyyar Arewacin kasar na samar da kashi 98 na tumaturin da ake amfani da shi kowacce sheka a fadin kasar.

Mr Iwejere, wanda ya bayyana hakan a wani taron kasa na shekara-shekara na masu ruwa da tsaki a harkar samar da tumatur, NTSS wanda na shekarar 2019 ya gudana a jihar Kano, cikin gidan gwamnatin jihar a ranar Alhamis, ya ce daga cikin jihohi 12, Kano ce tafi ko ina samar da tumaturi a shiyyar.

A cewarsa, wannan nasarar da jihar ta samu na samar da isasshen tumaturi ya janyo yawaitar samuwar ayyukan yi ga matasa a jihar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel