Ke duniya ina zaki damu? Wani Uba ya binne dan jariri da ransa a jahar Jigawa

Ke duniya ina zaki damu? Wani Uba ya binne dan jariri da ransa a jahar Jigawa

Rundunar Yansandan jahar Jigawa ta sanar da ceto rayuwan wani dan jariri da mahaifinsa ya binneshi da kansa sakamakon takaddama da ta auku tsakaninsa da tsohuwar matarsa, mahaifiyar yaron, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Wannan lamari ya faru ne a garin Birnin Kudu na jahar Jigawa, inda dan jaririn ya kwashe sama da sa’o’I goma sha biyu binne a cikin kasa, har sai da Yansanda suka kama mahaifinnasa daya nuna inda binneshi, suka cetoshi.

KU KARANTA: Daga gidan yari, tsohon gwamna Dariye ya nemi yan Najeriya su zabi Buhari a 2019

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar Yansandan jahar Kano, SP Abdu Jinjiri ne ya bayyana haka a ranar Litinin 4 ga watan Janairu, inda yace takkaddamar ta samo asali ne a lokacin da mahaifiyar jaririn, Hussanina Yusuf yar shekara 20 mazauniyar kauyen Tosawa ta kai karar cewa an sace mata jariri.

Daga nan Yansanda suka bazama neman wannan jariri, inda suka fara da yi ma Hussaina tambayoyi, wanda ta shaida musu cewa tsohon mijinta mai suna Ashiru Abubakar dan shekara 27 take zargi da hannu cikin bacewar jaririn nata.

Kaakaki Jinjir yace Abubakar ya saki Hussaini, amma duk da haka sai suka dinga haduwa suna saduwa da juna a boye, a haka har ta dirka mata ciki, a kokarinsa na boye labarin an haifa masa dan shege sai ya sulala dakin Hussaina, ya sace jaririn, kuma ya binneshi da ransa a cikin daji.

“Bayan mun kama Abubakar, sai ya yi mana jagora zuwa dajin daya binned san jaririn, muka kuma yi sa’a lokacin da muka hakoshi yana da rai, bayan kwashe sama da awanni 12 a cikin kasa kenan.” Inji shi.

Daga karshe Kaakaki Jinjiri yace a yanzu haka sun kama Ashiru da Hussaina, kuma sun kaddamar da bincike game da lamarin a babban ofishin Yansanda dake garin Birnin Kudu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel