Rigimar duniya: Wata kyakkyawar mata mai ciki ta damfari Dangote

Rigimar duniya: Wata kyakkyawar mata mai ciki ta damfari Dangote

Alkalin wata kotu ta musamman dake yanke hukunci akan laifuffuka dake zaman ta a Ikeja ta jihar Legas mai suna Mai shari'a Oluwatoyin Taiwo a ranar Litinin ta yankewa wata mata mai suna Judith Okonkwo hukunci bisa laifin damfara kamfanin Dangote.

Matar Judith da yanzu haka ke dauke da ciki mun samu cewa tsohuwar ma'aikaciyar banki ce da aka sakaya sunan sa kotun ta tabbatar da cewa ta damfari kamfanin sarrafa fulawa na Dangote watau Dangote Flour Mills zunzurutun kudade har Naira miliyan 19.

Rigimar duniya: Wata kyakkyawar mata mai ciki ta damfari Dangote

Rigimar duniya: Wata kyakkyawar mata mai ciki ta damfari Dangote
Source: UGC

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun budewa matafiya wuta a Zamfara

Legit.ng Hausa haka zalika ta samu cewa matar mai shekaru 43 a duniya kotun ta same ta ne da laifuffuka akalla 3 da hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta shigar.

Da alkalin Mai shari'a Taiwo yake yanke hukunci, mun samu cewa ya yankewa wadda aka samu da laifin hukuncin daurin shekara daya a gidan yari ko kuma zabin biyan tarar Naira dubu 100 a kan kowane laifi daya cikin ukun da ake tuhumar ta.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa tun farko hukumar ta Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta gurfanar da matar ne gaban kotun tare da wasu mutane uku da suka hada da Oyebamiji Adewale, kamfanin canjin kudade Wize Bureau De Change Limited da kuma Maduka Uchenna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel