Da duminsa: APC ta kwacewa PDP mambobi sama da 5,000 a jihar Adamawa

Da duminsa: APC ta kwacewa PDP mambobi sama da 5,000 a jihar Adamawa

- Rahotanni sun bayyana cewa akalla mambobin jam'iyyar PDP 5,000 ne suka fice daga jam'iyyar zuwa APC a karamar hukumar Ganye da ke cikin jihar Adamawa

- Shugaban jam'iyyar na jihar ya ce babu wani banbanci tsakanin tsoffin mambobin jam'iyyar da sabbin shiga, haka zalika jam'iyyar zata baiwa kowa fili domin taka irin rawarsa

- Alhaji Inuwa Samaila, ya ce sun sauya shekar ne saboda irin ci gaban da jam'iyyar APC ta kawo a karamar hukumar

Akalla mambobin jam'iyyar PDP 5,000 ne a ranar Laraba suka fice daga jam'iyyar zuwa jam'iyya mai mulki ta APC a karamar hukumar Ganye da ke cikin jihar Adamawa.

Alhaji Ibrahim Bilal, shugaban jam'iyyar APC a jihar, a yayin marabtar wadanda suka sauya sheka zuwa jam'iyyar a yayin kaddamar da yakin zaben dan takarar gwamnan jihar karkashin APC a garin Ganye, ya ce har yanzu kofar jam'iyyar a bude take na karbar sabbin mambobi.

A cewar sa, babu wani banbanci tsakanin tsoffin mambobin jam'iyyar da sabbin shiga, haka zalika jam'iyyar zata baiwa kowa fili domin taka irin rawarsa.

KARANTA WANNAN: Matafiya su hankalta: Ba a dasa Bom a jirgin Air Peace daga Abuja zuwa Legas ba - NAAF

Da duminsa: APC ta kwacewa PDP mambobi sama da 5,000 a jihar Adamawa
Da duminsa: APC ta kwacewa PDP mambobi sama da 5,000 a jihar Adamawa
Asali: UGC

Shugaban jam'iyyar ya yi kira ga al'umma da su yi aiki kafada-da-kafada domin tabbatar da nasarar jam'iyyar a dukkanin matakai a zaben mai zuwa.

Alhaji Jibril Gangjari, shugaban jam'iyyar na karamar hukumar, ya jinjinawa jam'iyyar bisa gina titin Mayo Belwa zuwa Toungo, kana ya baiwa gwamnan jihar, Mohammed Bindow tabbacin ruwan kuri'u daga al'ummar karamar hukumar a zabe mai zuwa.

Alhaji Inuwa Samaila, daya daga cikin wadanda suka sauya shekar ya shaidawa manema labarai cewa ci gaba da jam'iyyar APC ta kawo a karamar hukumar ya sa suka yanke shawarar sauya shekar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel