Neman Taimako: Hauwa Suleiman na bukatar aikin kwakwalwa domin ta rayu

Neman Taimako: Hauwa Suleiman na bukatar aikin kwakwalwa domin ta rayu

Hauwa Suleiman, mai shekaru 26 a duniya, kamar kowa, tana da mafarke-mafarken da take so su zama gaskiya, tana da burukan da take son ganin ta cika su a rayuwarta. Sai dai, matasiyar, wacce ta kammala jami'ar Abuja a fannin kwarewar tattali, ta kamu da wasu cututtuka na kwakwalwa, da suka hada da 'cerebral aneurysm', 'brain hematoma' da kuma 'anterior temporal lobe trophy',

Hauwa Suleiman, wacce ta kamu da cutukan kwakwalwa da suka shafi 'cerebral aneurysm', 'brain hematoma' da kuma 'anterior temporal lobe trophy', wadanda idan har ba ayi aiki aka cire mata su ba, zai iya haddasa mata shanyewar jiki, inda rayuwarta zata koma kashi 40, wasu lokutan kuma, yankewar jiki da gushewar tunani na iya sanadin ajalinta.

Babban tashin hankalin a wannan lokaci, abun tausayi da zubar da hawaye, shine yadda jini ya fara bubbugowa daga kwakwalwarta, wanda ke haddasa mata ciwon kai mai tsanani, da yawan suma.

Wannan lalurar dai ta Hauwa ta fara ne tun a watan Yulin 2018, a lokacin da aka garzaya da ita asibiti bayan shanyewar rabin jikinta. Bayan gwaje gwaje aka garzaya da ita asibitin Menhyia da ke kasar Ghana, inda ta samu kulawar likitoci kafin dawowarta Nigeria.

KARANTA WANNAN: Iyaye mata kuyi hattara: An gano sinadarai masu guba a cikin nafkin din yara

Neman Taimako: Hauwa Suleiman na bukatar aikin kwakwalwa domin ta rayu

Neman Taimako: Hauwa Suleiman na bukatar aikin kwakwalwa domin ta rayu
Source: Twitter

Sai dai bayan watanni biyu, Hauwa ta fara fuskantar matsalar suma akai-akai tare da gaza yin magana, inda aka kaita asibitin Aminu Kano, daga nan kuma aka kaita sashen kwakwalwa na babban asibitin kasa da ke Abuja inda aka yi mata gwaje gwajen matsaloli na 'tremors'.

A watan Disamba, ta sake komawa sashen kwakwalwa na wannan asibitin, inda aka tabbatar da cewa tana da cutar kwakwalwa ta 'aneurysm' bayan yi mata gwajin MRI. Haka zalika, bayan an gudanar da gwajin 'CT angiography' an gano Hauwa na dauke da cutar kwakwalwa ta 'hematoma' da kuma 'temporal lobe atrophy'.

Yar uwarta Binta Suleiman, ta bayyana damuwarta akan makomar Hauwa, amma ta yi addu'ar samun saukinta. "Mun yarda da ciwon Hauwa ya zama kaddara ce daga Allah, mu yanzu babbar damuwarmu shine Allah ya sa ta ci wannan jarabawa," a cewarta.

A halin da ake ciki yanzu, hanya daya ce kawai za a iya kawo karshen wahalar da Hauwa ta ke sha, shine ta hanyar da ake kira a turance 'endovosular coiling' wanda kuma ba a yinsa a Nigeria. Sai dai, a halin yanzu babu kudaden da za a gudanar da wannan aiki, wanda za a yi shi a Burtaniya (UK), kuma babu isasshen lokacin da za a bata.

Domin haka ne ake rokon daukacin 'yan Nigeria, masu hannu da shuni, da su taimaka da abunda Allah ya hore masu, wajen ganin an kai Hauwa Burtaniya domin yi mata wannan aikin, wanda kuma zai bata damar ci gaba da rayuwa tare da ci gaba da aikinta na likita.

Domin bada gudunmowarka ga Hauwa, an bude asusu a shafin 'Go Fund Me', a www.gofundme.com. Idan an shiga sai a nemi asusun 'Friends For Hauwa' a shafin, tare da bayar da tallafin da aka yi niyya.

Shiga shafin kai tsaye: https://www.gofundme.com/friends-for-hauwa?utm_source=facebook&utm_medium=social&utm_campaign=fb_dn_cpgnstaticsmall_r

Ko kuma a je banki kai tsaye ko ta hanyar aikawa ta wayar hannu zuwa ga:

Banki: GTBank

Lambar Asusu: 0164752200

Suna: Hauwa Suleiman

Allah ya bada ikon taimakawa Amin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel