Noma tushen arziki: Yadda Kano ta zama lamba daya wajen samar da tumatur

Noma tushen arziki: Yadda Kano ta zama lamba daya wajen samar da tumatur

- Emmanuel Ijewere, mataimakin kungiyar 'yan kasuwar kayan gwari ta Nigeria, ya ce Arewa na samar da kashi 98 na tumaturin da ake amfani da shi a kasar

- Mr Iwejere ya ce daga cikin jihohi 12, Kano ce tafi ko ina samar da tumaturi a shiyyar

- Tun farko a jawabinsa, sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a samar da kwararan matakai na bunkasa hanyoyin samar da tumaturi da kuma isarsa ga jama'a

Emmanuel Ijewere, mataimakin kungiyar 'yan kasuwar kayan gwari ta Nigeria, ya ce jihohin shiyyar Arewacin kasar na samar da kashi 98 na tumaturin da ake amfani da shi kowacce sheka a fadin kasar.

Mr Iwejere, wanda ya bayyana hakan a wani taron kasa na shekara-shekara na masu ruwa da tsaki a harkar samar da tumatur, NTSS wanda na shekarar 2019 ya gudana a jihar Kano, cikin gidan gwamnatin jihar a ranar Alhamis, ya ce daga cikin jihohi 12, Kano ce tafi ko ina samar da tumaturi a shiyyar.

KARANTA WANNAN: Yan Nigeria ba zasu gane sun yi kuskure ba sai sun sake zabar Buhari da APC a 2019 - Falae

Noma tsuhen arziki: Yadda Kano ta zama lamba daya wajen samar da tumatur
Noma tsuhen arziki: Yadda Kano ta zama lamba daya wajen samar da tumatur
Asali: Original

A cewarsa, wannan nasarar da jihar ta samu na samar da isasshen tumaturi ya janyo yawaitar samuwar ayyukan yi ga matasa a jihar.

Mr Iwejere, wanda shine kodinetan taron, ya ce manufar taron shine bunkasa hanyoyin samar da tumaturi da isar da shi ga jama'a da kuma gano matsalolin da ake fuskanta wajen samar da tumaturin da nufin samar da hanyoyin magance matsalolin domin ganin ya wadaci kasar baki daya.

Tun farko a jawabinsa, sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a samar da kwararan matakai na bunkasa hanyoyin samar da tumaturi da kuma isarsa ga jama'a.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel